Amfanin rake ga lafiyar jikin mutum ( kimiyya)
Kamar yadda kowa ya sani rake wani yar karamar bishiya ce da ake shukawa inda ruwa yake ko kuma nace wani kara ne mai kama da karan dawa saidai shi yafi karan dawa kauri nesa, sannan ya rabu kala kala wani za ka ganshi kalar jan duhu yayinda wani kuma kalarsa daya sak da karan dawa.
A ina ake samun rake?
Ko ina akwai rake a fadin kasar nigeria saidai hakan ba shine yake nuna ko ina ana shuka shi ba, a'a an same shi ne saboda yawan son da ake masa.
Rake ya samu matukar karbuwa agun mutane fiye da tunani saboda dadin da Allah ya hore masa in ana sha, to saidai ashe ba iya zakin da yake dashi bane kawai amfaninsa yana magunguna da yawa ta kuma bangarori daban daban.
Abinda masu bincike suka ce akan rake
Masu bincike akan rake sunyi bincike kuma sun gano wasu magunguna da rake yake yi ga jikin dan Adam masu yawa kuma masu amfani domin bangaren da yake amfanin suma wasu sassa ne da suke da matukar mahimmanci ga jiki domin idan wadannan sassan suka samu matsala to mutum yana cikin gagarumar matsala.
Maganin da rake yake
Idan mutum yanada ciwon hanta ana son yana yawan shan rake domin yana rage cutar sosai fiye da tunani.
Masu bincike sunce yawan shan rake kan kare mutum daga cutar ciwon hanta dan haka ake da bukatar mutum yana yawaita shan sa akai akai.
Sannan yawan shan rake yana taka rawar gani wajen magance matsalolin da suka shafi mafitsara.
Sannan yana taimakawa wajen saka koda tayi aiki mai kyau.
Comments
Post a Comment