Min menu

Pages

 Amfanin Ruwan dumi ga jikin mace



Shan ruwa mai yawa yanada matukar amfani da mahimmanci ga jikin dan adam mace ko kuma na miji, domin yakan sa sassan jiki suyi aiki ba tare da an samu matsala ba, to saidai ruwa mai dumi yafi matukar mahimmanci ga jikin dan adam fiye da ruwa haka.

Domin shi yana taimakawa sosai wajen saka abinci ya narke da wuri maimakon ruwa haka, dan haka mafiya yawan masu bincike sun nuna ruwa mai dumi yafi amfani sosai fiye da sauran ruwan musamman wanda yake da sanyi.

Sannan yawan shan ruwa a kullum ya danganta ne da girman mutum da kuma nauyinsa ko kuma yanayin gurin ko kuma muhallin.

Gaba daya dai shi ruwa mai dumi bashi da wani damuwa ko matsala ga jikin mutum, sannan yana kara lafiya tare da kare jiki daga kamuwa da cututtuka, saidai mutum ya zama ya kare kansa daga shan ruwa wanda yake da tsananin zafi domin masu bincike sunce shan ruwa mai tsananin zafi ko kuma shan abu mai matukar zafi kan kawo damuwa ga cikin jikin mutum da kuma kayan cikinsa.

Dan haka dai shan ruwa mai dumi yanada matukar amfani sosai dan haka ga kadan daga cikin wasu abubuwa da yawan shan ruwa yake kawowa ga jiki.

* Na daya shan ruwa mai yawa musamman na dumi yana karawa kayan ciki lafiya domin yakan zagaya tare da kawar da duk wasu abubuwa.

* Shan ruwa mai yawa yakan taimakawa kwakwalwa.

* Shan ruwa mai yawa yana taimakawa wajen rage nauyin jikin mutum.

* Kuma yakan taimaka wajen kawar da yoyon hanci.

* Sannan shan ruwa mai dumi kuma mai yawa yana taimakawa wajen zagayawar jini a jiki.


Dan haka shan ruwa yanada amfani sosai kuma yanada fa'ida dan haka muna shan ruwa a koda yaushe domin samun lafiyar jikinmu.

Comments