Min menu

Pages

An tsinci gawar wata ma'aikaciyar gidan radio

An tsinci gawar wata ma'aikaciyar gidan radio



Tunda rana ta fadi sai wani hadari mai karfi ya gangamo, wasu bakaken gajimare masu gudu suka lullube sararin samaniyar, wannan yasa nan da nan garin yai duhu. Aka fara kada iska mai karfi wanda tasa bishiyoyi suka dinga rangaji, duk wannan iskar da ake mutanen dake cikin wannan gidan radion basu sani ba kasancewar gidan radion irin rufaffen nan ne wanda in mutum yana ciki to da wuya yasan abinda yake wakana a waje, inka dauke farfajiyar gidan radion wanda shine kadai bai zamto a rufe ba.

Wani gidan radio

Gidan radio ne tsararre mai matukar kyau wanda aka aiwatar da gininsa ba ganda, duk kuwa da cewar ba wani kato bane na kuzo ku fada, hawa biyu ne da gidan radion a hawa na farko shine inda mafiya yawan ofisoshin da ma'aikatan gidan radion suke,  sannan anan duk wasu baki da masu ziyara suke gabatar da al'amuransu na yau da kullum,  yayinda hawa na biyun kuma anan duk wasu manyan office-office suke kuma anan ake watsa dukkan wasu shirye-shirye tare da tacewa. Akwai abin birgewa matuka gamida ban sha'awa ga gidan radion duk da kasancewarsa karami, amma ya samu matukar karbuwa  domin suna watsa shirye shiryensu masu matukar kyau da ma'ana wanda suka shafi bangarori mabambata, sannan akwai ma'aikata masu hazaka da tsananin kwarewa.

Wacece Farida Bala?

Farida Bala matashiyar yar jarida ce kuma ma'aikaciya a wannan gidan radion wanda take gabatar da shirin KASARMU A YAU. Shirin ya samu matukar karbuwa agun al'umma domin shiri ne wanda ake gabatar da abubuwan da suka shafi kasarmu da kuma yadda yan siyasa da manyan ma'aikata da kuma jami'an tsaro suke cin karensu babu babbaka a wannan zamanin wanda talaka yake cikin wani hali na kaka-ni-kayi ko kuma nace halin ni yasu tare da danniya gamida nuna halin ko in kula daga gurin shugabanni walau masu mulkin siyasa ko kuma sarakunan gargajiya dadai sauransu, sannan shirin yafi maida hankali gaba daya akan manyan matsalolin da suke faruwa a kasa musamman arewa, sannan yana haskawa mutane hanya wajen nuna musu duk wasu matsaloli da suke faruwa a kasa akwai sa hannun manyan yan siyasa da kuma manyan sarakuna tare da hadun bakin manyan jami'an tsaro, wannan yasa shirin yake da matukar farin jini agun al'umma musamman talakawa wanda kaso masu yawa sune a wannan kasar tamu, domin da zarar lokacin fara gabatar da shirin ya kusa to kusan ko ina zaka iske radio a kunne, hatta majalisa gun taruwar mutane, sukan kunna radion musamman domin sauraron shirin na kasarmu a yau. Sauran shaguna da kuma rumfunan masu shayi da sauran kayayyakin sayarwa na yau da kullum su dama gurinsu cika yake yi domin sauraron shirin.

Sau biyu ake gabatar da shirin a sati da ranar litinin sai kuma ranar juma'a, duka lokaci guda shirin yake zuwa karfe takwas daidai na dare. 

Kowa ya shaidi Farida Bala wajen aiki da kwarewa da kuma fadar gaskiya komai dacinta, bata tsoron sanar da mutane duk wasu al'amura da suke faruwa a kasa, sannan babu ruwanta duk wanda shirin da take ya biyo ta kansa zata fadi duk abinda yayi walau na alkhairi ko kuma rashinsa, hakan yasa mafiya yawan yan siyasa masu gaskiya suka ninka abubuwan alkhairin da suke kuma tauraruwarsu taci gaba da haskawa a ko ina mutane suka dinga fadar alkhairansu, yayinda azzaluman yan siyasa marasa adalci suka zama abin kyama da zagi daga wajen al'umma, sannan suka daina zabensu koda sun fito takara hakan yasa tauraruwar da yawa a cikinsu ta dushashe ta daina haskawa. Yar jarida mai aiki da gaskiya haka mutane da yawa suke fada mata a dalilin gaskiyarta. Wannan yasa take yawan samun yabo daga gurin al'umma gama gari, domin ta samu manyan kyaututtuka da kuma lambobin girmamawa daga gurin tarin mutane masu radin kwatanta gaskiya, domin ko kwanan nan saida ta karbi wata lambar yabo daga kungiyar hadin kan matasa. Yayinda a daya bangaren take fuskantar matukar kalubale musamman gurin yan siyasa da kuma gurbatattun mutane wanda basu da gaskiya saidai duk da haka bata taba jin tsoro ko kuma ta daina aikata aikin da take na fadar duk wata gaskiya idan har akan aikinta na jarida ne ko.

A gaggauce ta shigo cikin gidan radion kasacewar lokacin gabatar da shirin da take jagoranta ya kusa, haka kuma dole tayi sauri domin kar wannan hadarin daya gangamo ya sauko ya sameta bata karasa cikin gidan radion ba wanda hakan ka iya sa ta bata lokaci bata jeba.Tana zuwa shigewa kawai tayi domin gate din gidan radion a bude ta ganshi ba kamar sauran ranaku ba wanda sai tayi horn da motarta sannan mai gadi zai bude mata ta shiga. Bayan ta adana motar ta a inda ta saba ajiyewa sai kuma ta nufi inda office dinta yake a hawa na farko domin ta shirya yan wasu takardun da zata gabatar da shirin dasu, tana zuwa kofar office din saita dauko yan makullanta da suke cikin yar karamar jakar dake hannunta wanda a cikinsu akwai na kofar wannan office din domin ta bude kofar office din dashi, saida taje sakawa a kofar inda dan makullin yake, tana dafa kofar sai taga kofar  ta bude, abin ya bata mamaki da taga kofar a bude, ta dan tsaya tana wasu yan nazarirrika da tunane tunane daga karshe tai tunanin watakila wanda da yake musu share share ne ya manta bai kulle kofar ba bayan ya share office din, taso juyawa ta koma domin taje bangaren da masu sharar suke sai kuma ta fasa saboda sauri take domin lokacin gabatar da shirin da take jagoranta na kasarmu a yau ya kusa, ta maida dubanta sauran office biyun dake can nesa kadan da inda office din nata yake amma sai taga duka suna rufe, ba wani abin mamaki bane don hakan ta faru domin masu zama a office din dama tun karfe shida na yamma suke rufewa. Wannan yasa ta tura kofar office din nata ta shiga abin ya bata mamaki da taga office din da duhu domin ita dai tasan koda wanne lokaci fitilar a kunne take barinta amma babu mamaki mai sharar ne ya kashe, don haka ba tare da bata lokaci ba ta mika hannunta gurin da makunnar lantarkin take ta kunna, take office din ya kaure da haske sai a lokacin tai ido biyu dasu wanda suke a tsaye kamar gumaka wasu manyan karti ne guda biyu majiya karfi. Tai saurin ja da baya da niyyar ta fice daga office din amma sai ta kasa sanadin ji da tayi dayan ya fisgota gamida makata da jikin dakin tun kafin tai wani motsi ta sake jin saukar faskeken hannunsa a wuyanta ya shake ta zai kasheta nan fa ta fara kokarin kwatar kanta ta ko wanne irin hali ta miko hannunta domin ta banbare hannunsa amma taji ta kasa sai a lokacin ta tuna da dan karamin almakashin dake jikin yan makullan dake rike a daya hannun nata tai saurin jawoshi sannan ta cakawa mutumin daya riketan da dukkan karfinta jini yai tsartuwa daga inda almakashin ya huda, ta sake soka masa a karo na biyu, bata samu damar cire almakashin ba sanadin karar da wuyanta yayi a karo na karshe...

Tunda aka tsinci gawar ma'aikaciyar gidan radion farida bala sai abubuwa suka rikice suka rincabe musamman a cikin garin, ko ina in banda labarin mutuwarta babu abinda ake fada, hankulan jama'a yai kololuwar tashi na samun mummunan labarin kisan da akaiwa farida, nan fa mutane da dama wanda suke kusa da gidan radion suka fara dafifin zuwa kofar gidan radion domin su ganewa idanunsu abinda yake faruwa saidai duk wanda yaje dole ya tsaya domin bazai samu ya shiga ba sanadin jami'an tsaron da sukaiwa gurin kawanya wannan tasa bakin gidan radion ya cika sosai da jama'a kowa na fadar albarkacin bakinsa wasu na ganin shirinda take gabatarwa ne yasa aka kasheta wasu kuma na cewa wanda yai kisan yanada wata manufa akanta shine yasa ya kasheta,  nan dai kowa ya fara fadin albarkacin bakinsa game da mutuwar yar jaridar mai tashe kuma ma'aikaciyar gidan radion farida bala. Asp yahuza hamza shine jami'in dan sandan yake jan ragamar binciken kisan da akaiwa ma'aikaciyar gidan radion kuma yar jarida farida bala, a wata majiyarma ance shine saurayinda zai aureta wata uku masu zuwa kuma gashi an kasheta. 

Asp yahuza hamza tare da sauran yan sanda biyu ne suka samu suka shiga office din da gawar farida bala din take,sai kuma daya daga cikin masu aiki a gidan radion, asp yahuza hamza ya karewa gawar farida bala dake kwance kallo na dan wani lokaci kamar yana tunanin zata tashi, ga jini nan ko ina a watse a kasa cikin office din saidai babu wani guri haka a jikinta da zai nuna harbinta akayi ko kuma wani abu aka soka mata,sannan ya kawar da kansa ga inda gawar take ya kalli ma'aikacin gidan radion sannan ya fara masa magana da cewa ina fatan babu wani daya tabata? Eh babu wanda ya tabata, ya bada amsa a takaice. Akwai abin mamaki ga wannan kisan, domin ga jini nan a kasa saidai babu wata alama ta harbi ko sukar wuka dan haka akwai iyuwar faruwar wani abu, dan haka kofur bashari ka tsaya anan ni kuma dani da Sargent ya'u zamu fita zamu zo da likitan da zai mana bincike domin tabbatar da wannan jinin. Yana fadar haka ya juya ya fice daga office din, dan sanda dayan ya take masa baya suka fice daga cikin office din suka shiga inda harabar gidan radion take. Asp Yahuza Hamza ya dubi sauran yan sandan dake tsaye a kowanne bangare na cikin asibitin sannan yace koda wasa kada ku bari wani ya fita daga cikin gidan radion nan, sannan biyu daga cikinku suje su zomin nan da wanda yake gadin wannan gidan radion yanzu ina jiranku domin akwai tambayarda zanyi masa. Yan sandan biyu suka tafi da sauri zuwa inda dakin da mai gadin yake wanda yake can manne kusan kofar shigowa gidan radion, babu jimawa sai gasu sun fito da sauri, basu gama tsayawa ba sanadin tambayar da asp yahuza hamza yai musu da cewar yana ina? An kashe shi, ta hanyar daure masa wuya da igiya sannan kuma an daddaure hannu da kafafunsa shine amsar da suka bayar lokaci guda cikin hadin baki. 

An kashe shi? Asp Yahuza Hamza ya tambaya a kidime. Lalle koma waye yai wannan kisan yanada wayo wato ya kashe mai gadin ne domin kar ya bada labarin yaga shigowarsu ko kuma yace ya gane su domin haka yasa suka kashe shi shima, ya daga kansa ya karewa gidan radion kallo tun daga kofar shigowa gidan har zuwa harabarsa ya tsayar da kallonsa ga wata yar karamar camera dake makale can a jikin dogon ginin kusa da kofar shiga ainashin cikin gidan radion tana kallon duk wanda zai shigo, yai nuni da hannunsa inda camerar take a makale sannan ya kalli  sauran mutanen gidan radion da suke tare a gu daya suna zaman jiran binciken da ake yi na mutuwar abokiyar aikinsu farida bala cewar waccen ai CCTV camera ce da fatan tana aiki? Ya kare maganar tasa da tambaya. Eh tana aiki sosai ma kuwa daya daga cikin mutanen ya fada ga dukkan alamu shine yake kula da bangaren cctv camerar. Asp Yahuza Hamza yace zanso muje yanzu inda bangaren da computer dake jone da cctv camerar domin akwai iyuwar ta dauki dukkan abubuwan da suke faruwa tun daga safiya zuwa yanzu, dan haka waye ma'aikaci a bangaren ina nufin wanda yake kula da bangaren? Mutumin da yai magana da farko ya daga hannunsa sannan yace nine nake kula da bangaren dan haka muje na kaika inda office din nawa yake, ya fadi maganar lokacinda ya fito daga cikin taron mutanen da suke gurin ya tsaya can nesa kadan da inda Asp yahuza hamza yake. Dan kallonsa kawai yayi nadan wani lokaci sai kuma ya kawar da kansa daga gareshi sannan ya sake duban wani gajeran dan sanda dake tsaye yanata muzurai shi kadai yace kai kuma kafin na fito ka tabbatar kaje kunzo min da likitan da zai gwada wannan jinin, bai jira ya saurari maganar da gajeran dan sandan ya bashi amsa ba sai kawai ya dubi inda mutumin da zai kaishi inda dakin da computer da zasuyi bincike take yai masa alama suka tafi. Ba wata doguwar tafiya sukai ba suka isa gurin bayan sun karasa gurin da computocin suke sai kawai mutumin ya kunna wata babbar computer wanda itace cctv camerar take jone a jikinta, nan take saiga duk kan abubuwan da suka faru cikin wannan gidan radion suna bayyana sahu sahu ko kuma ince daya bayan daya, har aka zo kan wasu manyan bakaken mutane mutane guda biyu da suka shigo a cikin wata bakar mota mai bakaken gilasai, wanda suna zuwa bayan an bude musu gate basu ko lura da inda mai gadin yake ba sai kawai suka nufi inda dakinsa yake, ganin wadannan mutanen sun nufi dakinsa harma sunkai ga shiga yasa ya bisu ciki da gudu, bayan dan kankanin lokaci sai gasu sun fito da sauri, bayan sun danyi dube dube sun tabbatar babu wanda ya gansu sai kuma suka shige da gudu gudu cikin gidan radion bayan dan kankanin lokaci da shigewar tasu saiga motar farida bala tazo, sai kuma ta ajiye motar tata ta shiga cikin gidan radion, babu jimawa saiga wadannan kartin biyu sun fito da gudu a daidai lokacin ne ruwan sama tamkar da bakin kwarya ya sauko akayi walkiya da rugugin aradu, suka karasa gunda motarsu take suka shiga tare da bata wuta suka fisgeta sukai waje da gudu. Asp Yahuza Hamza yai saurin mikewa da sauri kamar wanda yake tunanin wani abu ya nufi gunda dakin da gawar yar jarida farida bala take ya shiga, sai a lokacin yaga wasu yan makullai a karkashin tebur din dake jikin office din suma duka jini ya bata su, ya dubi dan sandan da ya bewa jiran gawar sannan yai masa nuni da yan makullan sannan yace ina fatan baka tabasu ba?  Eh ban tabasu ba domin banma lura da gurin ba saidai akwai wayarta da ake ta famar kira tun dazu. Ina wayar tata take? Asp Yahuza Hamza ya tambaya, tana cikin cikin waccan jakar yai masa nuni da inda jakar take acan karshen office din a yashe. Sannu a hankali ya taka ya karasa inda jakar take ya dauketa sannan yasa hannunsa ya dauko wayar a lokacin ne sukaji an turo kofar office din, mutum hudu ne suka shigo a tare biyun mata da miji ne kuma sune mahaifan yar jaridar farida bala, sai kuma sauran biyun wanda sune wannan gajeran dan sandan da kuma likitan da yazo dashi. Hajiyar dake cikin mutanen ta fashe da kuka tun bayan da taga yarta a kwance bata motsi sannan ta fara surutai tana cewa dama ya fada cewar saiya rama abinda tai masa shine kuma saiya kasheta wallahi bazan yadda ba sai anbi min hakkin yata ta sake fashewa da kuka. Asp Yahuza Hamza ya dubi hajiyar da take ta famar rusa kukan sannan yace akwai wani da suka samu sabani ne dashi? Eh akwai hajiyar ta fada lokacinda ta danyi shiru da kukan da take sannan tace akwai wani tsohon saurayinta wanda yake kaunarta tun tana karama kuma shine ya dauki nauyin kusan komai nata hatta karatun nan nata ma shine ya dauki nauyi to bayan ta gama ne tace ita bata sonsa suka rabu dashi baram baram yana cewa sai ya dau mataki akanta, hajiyar ta sake fashewa da kuka bayan takai karshe a maganar tata. Asp Yahuza Hamzan yace to shidin wannan saurayin nata dan ina ne kuma yana ina yanzu? Ya kare maganar yana daddanna wayar marigayiya farida balan dake rike a hannunsa watakila akwai binciken da yake a wayar. Sunansa Abdulraheem kuma dan cikin garinan ne alhajin ya sako bakinsa a karo na farko tun zuwansu cikin office din da aka kashe yar tasa farida. Asp yahuza hamza ya dubi likitan da tunda suka shigo dazu yake ta famar gwaje gwaje yace dashi Dr da fatan binciken yana tafiya daidai ina nufin ka gano abinda akai mata ta mutu,  dr ya dago da kansa sannan yace eh batun mutuwarta na gane anyi amfani ne da karfi domin wuya aka karya mata sannan wannan jinin ba daga jikinta ya fita ba domin babu wani guri da ya nuna hakan sannan zanen hannun dake jikin wannan almakashin ya nuna zanen tambarin hannun marigayiya ne saidai jinin ban gane kona waye bane amma ina tunanin itace ta sokawa wanda yazo kashetan lokacinda take kokarin kwatar kanta daga gareshi. Asp yahuza hamza ya gyada kai alamar gamsuwa da maganar da likitan yace sannan ya dubi yan sanda biyun dake tsaye yace kuyi sauri kuje da mota ku nemo duk inda wannan Abdulraheem din yake har yanzu dai wayar na hannunsa saidai a yanzu ya kara wayar ne a kunnensa yana sauraron wani abu, bayan dan lokaci sai ya dauke wayar a kunnensa sannan ya dubi mahaifan farida bala din da kuma likitan sannan yace insha Allahu zamu samu nasara a wannan binciken domin yanzu haka na saurari wani recording ne daga wannan wayar wanda naji wasu zantuka da kuma gargadi daga wani mutum cewar a kada ta sake gabatar da wannan shirin da tace zatayi yau akan yaudarar da wasu yan siyasa suke yi daga karshe ya nemi zai bata kudi ko nawa akan ta boye wannan abin amma taki yadda da batunsa, yai iya yinsa amma shiru wannan ne yasa da yaga bata amince ba kuma bata da niyyar amincewa da bukatarsa shine yasa ya fara mata mummunan gargadin da cewa zai kasheta ya zama ajalinta, ya sake kunna recording din a karo na biyu sauran mutanen dake office din suka saurara, mahaifiyar farida bala ta sake fashewa da kuka lokacinda recording din yakai karshe sannan ta fara magana muryarta na rawa tace lalle sai Allah ya saka mata kan wannan kisan da akai mata kuma insha Allahu shima wanda yai wannan kisan bazai gama da duniyq lafiya ba tunda zalunci ne aikinsa, ta sake fashewa da kuka gamida durkushewa a kasa kusa da gawar da yarta farida bala take. Asp Yahuza Hamza ya dubeta sannan yace karki damu mama nayi alkawarin duk da wani wanda keda hannu cikin wannan kisan saina kamo shi kuma sai an yanke masa hukunci daidai da laifin daya aikata koshi waye haka kuma ko wanne mukami ne dashi a wannan gwamnatin koda zan rasa aikina domin bazai iyu ana gani irin wadannan gurbatattun mutanen suna cin karensu ba babbaka a cikin al'umma ba. 

KAMMALAWA 

Tunda mutane sukaji labarin sanata Sani kashim ne yasa aka kashe ma'aikaciyar gidan radion farida bala sai surutu ya kaure kowa na fadin albarkacin bakinsa wasu na cewa dama tace yau zata fasa kwai wanda hakan zaisa a gane gurbatattu daga cikin yan siyasa, inda wasu kuma banda tsinuwa babu abinda suke masa. Daga karshe aka wanke Abdulraheem cewar bashi da laifi kuma ba shine ya kashe Farida Bala ba sannan sannan kuma Asp yahuza hamza tare da sauran mutane da kuma gidajen radio da jaridu sun taka rawa sosai ganin an hukunta wanda ya dauki nauyin wannan kisan da akaiwa ma'aikaciyar gidan radion farida bala tare da tara mai yawa sannan suma mutanen da aka biya sukai wannan kisan aka kamo su tare da yi musu hukunci mai tsanani wanda ya dace da irin laifin da suka aikata. 

Wannan shine karshen wannan labarin na gode sosai.

Daga Abdulraheem yusuf bulangu 08081868923

Comments