Min menu

Pages

Bukola saraki ya magantu akan abubuwan da suke faruwa a Nigeria

 Bukola saraki ya magantu akan abubuwan da suke faruwa a Nigeria



Tsohon dan siyasar nan da yayi suna wanda kuma yai mulki a lokacin PDP Bukola Saraki ya magantu akan abubuwan da suke ta famar faruwa a kasa, yace yanada kyau a ajiye batun siyasa a gefe ko kuma batun addini azo a hada kai don ganin an kawar da wadannan abubuwan dake ta famar faruwa marasa kyau a Nigeria.

Da yake bayaninsa a wani shafi nasa na watsa labarai a yanar gizo yace, yin shiru ga irin wannan abubuwan shine yasa kasar ke ta famar tabarbarewa har yanzu an kasa gyarota.

Ya kara da cewa dole ne yan kasar su hada kansu guri guda dan kawar da rigimar kabilanci da kuma ta addini hakan shine zai taimaka kasar ta kai inda ake so takai.

Bukola sarakin ya nuna damuwarsa matuka ga abinda yake faruwa yanzu tsakanin makiyaya da kuma wasu daga cikin mutanen Ondo da Oyo, har yake danganta abin da rashin hadin kai ko kuma nuna kabilanci,domin da akwai hadin kai a kasa da haka bata faru ba a cewarsa.

A yan kwanakin nan labarai sai zuwa suke ta gurare da dama akan tashin fulani makiyaya da gwamnatin Jihar Ondo ke shirin yi wanda hakan ke neman tada kura, domin har an fara yamutsa gashin baki tsakanin kungiyar miyatti Allah da wasu mutane.

Wanda in ba ai da gaske ba sai abubuwan suzo suyi rashin dadi, wanda kowa zaizo yana dana sani.

Bukola Saraki ya kara da cewa, mutane suyi karatun ta nutsu su ajiye duk wani batun siyasa ko kabilanci ko banbancin addini suzo a kai kasar nan tudun tsira.

Sannan kuma ya sake jan duk wani mai fada aji dake fadin wannan kasa akan su hadu a zauna domin a shawo kan wannan matsalar dake ta famar faruwa a kasa.

Comments