Min menu

Pages

Idan aka bincika tun a 2014 yawancin yan Nigeria ba cikakkun yan kasa bane

Idan aka bincika tun a 2014 yawancin yan Nigeria ba cikakkun yan kasa bane



Abin mamaki da ban haushi bazai taba karewa ba a Nigeria, a kullum a Nigeria abubuwa kara damulewa suke ta yadda a duk lokacin da mutum mai ilimi yayi shiru yana nazari saiya gano gibi da tawaya mai karfi irin Wanda idan aka barta wata rana sai ta zama karfen kafa. 

Wani matashi mai suna Bashir Bab a Nigeria ya koka ta yadda abubuwa a suke yiwa maras kudi wahalar samu koda kuwa hakkin sane daga wajen hukuma, Matashi Bashir Bab yace a  Nigeria mafi akasarin abubuwan da suka shafi talaka wahalar tabbata yake, ko kuma kafin abu ya sami mutum talaka saiya kusa ya hakura.

Ya kuma kara da cewa duk da ana samun irin wadannan matsaloli shuwagabanni basa  taba yarda abubuwan da suka shafesu su tsaya cak kamar yadda yawancin abubuwan da suka shafi talaka basu da matukar daraja matsawar abin bazai shafi shugaba ba, Misali katin zabe da Katin shaidar zama Dan kasa. Idan aka dubi katin zabe abu ne Wanda yake da sauki mutum ya sami cikakken katin zabe a Nigeria kuma a cikin sati daya ko biyu, kuma koda mutum talaka ne, ko kuwa ba'a lokacin zabe bane sabanin katin zama cikakken dan kasa.

Bashir Bab yace tun 28 ga watan Augustan shekarar dubu biyu da sha hudu (2014),  aka kaddamar da sabon kalar katin dan kasa mai  lamba (NIN Number) Wanda akeyin amfani dashi a yanzu a zamanin mulkin Dr. Good luck Ebele Jonathan. Bashir yace daga lokacin da aka kaddamar dashi kawo yau  katin zama Dan kasa har yanzu bai wadata ba saboda karancin masuyin aikin katin kamar yadda ake daukar isassun masu yin katin zabe, a lokaci guda kuma ta wani bangaren kamar hukuma bata damu da yan kasar su zama 'yayanta ba. 

Bab ya kara da cewa Idan kuma aka koma bangaren wadanda suka riga suka sami rigistar katin zama cikakken Dan kasar suma mafi akasari katin bana din-din bane (Temporary), Don haka wannan al'amari tawaya ce babba ace katin zama dan kasa na din-din yana wahalar samuwa ga dan kasar da a kalla yakai shekara 20 zuwa sama amma kuma sai a sami Dan shekara 18 ya mallaki katin zabe na din-din. Kuma ba komai bane ya kawo haka a iya fahimtata face katin zabe a bune Wanda ya shafi zabar shugaba shi kuma katin zama Dan kasa talaka ne kawai rashinsa ke kalubalanta, don haka akan katin shedar zama cikakken dan kasa duk mai temporary ba cikakken dan kasa bane.Bab ya kare zancensa Da cewa ina shawartar mahukunta dasu maida katin zabe ya koma na dan kasa haka kuma yaci gaba da zama ana zabensa.


Comments