Idan har ka kasance kana aikata zina to irin haka ce zata faru dakai.
Yana kuka ya fara magana da cewa;-
Tun da farko maganar abokaina da sauran mutanen da muke zaman mutunci na tuna, basu kadai ba harda ta sauran yayuna da kanne na.
Ko kadan bana lura da abinda suke fada domin a lokacin giyar samartaka da kuma kudin dana samu sune suke dibana, bana tunanin akwai wata rana da zata zomin nayi dana sanin abinda nake aikatawa.
Ban damu ba zan iya bewa mace ko nawa ne domin nayi taraiya da ita, hakan yasa naiwa mata da yawa ciki da yawa a cikinsu an zubar wasu da dama kuma sun haife kayansu, saidai daidai da rana daya ban taba karbar yaro daya da sunan nawa ne ba saboda ina amfani da kudi koda a kotu ne.
Mata da yawa cikin da nayi musu shine silar mutuwarsu wasu kuma sun shiga yawan duniya.
Abinda kayi dole za ai maka irinsa abokina musamman ma zina wanda ita bashi ce haka annabi yace maganar da abokina kabir kenan ya fadamin wata rana bayan munyi baram baram da wata yarinya da tazo tace nayi mata ciki.
Banyi dana sanin haka ba sai da tsufa ya fara zo mini kuma gashi na tara yaya mata sama guda tara, bawai yawan yayan dana tara sune sukafi damuna ba a'a ganin biyar daga cikinsu anyi musu ciki, wasu sau biyu wasu uku.
Abinda yake daure min kai shine har yanzu banji ance ga daya data samu mijin da zai aureta ba gashi wasu har sun fara fita daga tsarin da za a kirasu da yan mata.
Sauran hudun da suka rage basuyi cikin ba naji ana rade radin sun fara biyewa sauran yayun nasu, hakan yasa yanzu da matata take da ciki nake tsoro domin inna tuna abinda nayi a baya sai naji gabana Yana faduwa domin kar wanda za a haifa shima ya zama me irin halin sauran.
Sai yanzu dana sanin abinda na aikata ina saurayina ya fara shiga zuciyata, dana sanin da bazai amfaneni da komai ba gashi kuma sauran mutanen da suke bani shawara a wancan lokacin sunyi nesa dani wasu ma sun jima da mutuwa bare na koma gunsu ko zasu sake bani shawara.
Sauran matan dana batawa rayuwarsu da dama ban sake ganinsu ba bare na nemi afuwarsu wasu da dama sun mutu da bakin cikin abinda nai musu.
Wannan shine sakamakon abinda na aikata musu Allah ya fara saka musu tun a duniya.
Wannan dan karamin labarine dana rubuta gareku masu wannan halin domin hakan zata iya kasancewa a kanka kaima me irin wannan halin.
Comments
Post a Comment