Kasusuwan da sukafi kowanne kankanta a jikin mutum
Kasusuwa suna daga cikin mahimman siffofi wadanda suka hadu suka Samar da zubin halitta mai dauke dasu,domin kuwa haduwar kasusuwa daga kan daya (1) har zuwa Dari biyu da shida (206) ne suka Samar da adadin kasusuwan dake jikin kowane lafiyayyen mutum.
Duk da yake masana kimiyyar siffar halittu sunyi bayanin cewa akwai yan Adam masu kasusuwa a jikinsu sama dari uku amma jarirai ne wadanda basu wuce watanni uku da haihuwa ba, binciken ya nuna cewa a watannin farko na haihuwar mutum akan haifeshi ne da kasusuwa sama da dari uku Wanda daga baya wasu suke narkewa, wasu kuma su hade da wasu su bayar da adadin da ake dasu, karin wani binceken kuma ya bayyanar da cewa akwai mutane wadanda ake haifarsu da Karin wasu kasusuwa (mutane wanda aka Haifa da matsalar tawaya ko Karin hallitta ) kamar kashin hakarkari su karu su zama ashirin da shida (26) a maimakon 24 da kowane mutum keda su walau mace ko namiji.
Kasusuwan dake a jikin mutum siffofinsu sun bambamta daga babba zuwa karami daga dogo zuwa gajere daga faffada zuwa siriri ko mai tsini. Anan sashen kimiyyar wannan gida kai tsaye zaiyi duba ne akan kasusuwan da sukafi kowane kashi kankanta a jikin mutum.
Kasusuwa da sukafi kowane kashi kankanta a jikin mutum guda uku ne kamar haka:
1) Incus (makera)
2)malleus (Guduma)
3)stapes (likkafa)
Wadannan kasusuwan gaba daya a kunne suke kuma ana kiransu da ossicles a turance, wadannan kasusuwa suna da kaso mafi girma wajen karbar sauti ga wajen kunne tare da mikashi zuwa cikin ruwan kunne shi kuma ya karba ya baiwa jiniyoyin bada bayanai na sauti zuwa kwakwalwa domin ta tantance kalar sautin da ya wakan
Mu hadu a shiri na gaba domin sake samun wasu sabin shirye shiryen mu
Comments
Post a Comment