Ci gaban labarin
Banyi masa musuba na mika masa dan makullin motar na koma gefe na tsaya ina kallonsa ya tada motar sannan ya bata wuta lokaci guda yasa mata giya ya fisgeta baiko dubi inda nakeba ballantana har yaga hannun da nake ta famar daga masa.
Innan a tsaye har saida na daina hango danjar motar tasa sannan na shiga gida, kasancewar dakina a bakin kofa yake sai kawai na shiga ban tsaya bata lokaci ba na cire sabin kayan nawa na ajiye a gefe guda dan kar karin gugar nasu ya baci dan kuwa dasu nake sa ran komawa gun husna gobe.
Bayan na saka tsofin kayana sai kawai nai tsalle na hau kan tsohuwar katifata kura ta turnike kamar ana sukuwar dawakai nanfa gadon bayana ya sage saboda buguwar da nayi a jikin busheshshiyar katifar tawa bansan lokacin da nayi kara gamida mikewa tsayeba.
Na dade a tsaye bayana a sankare kamar wanda aka dakeni da sanda sannan na samu bayan nawa yadan dawo saiti.
Na dan karasa inda katifar take na hau cikin sanda dan gudun abinda taimin dazu na jingina da bango ina tunani da nazarin yadda soyayyata zata kasance da husna a haka har bacci ya zagayo ya daukeni..
Zafin ranar gamida haskenta suka doki fuskata nai sauri na tashi daga nannauyan baccin da nake naga ashema gari ya waye har rana ta fito, abin yayi matukar bani mamaki saboda wannan makarar da nayi dan kuwa ni iya sanina nasan na kai shekara uku ban makara irin yauba..
Nai sauri na mike daga kwancen da nake sannan naje nai alwala nai sallah...
Bayan la'asar tayi munyi sallah naje nai wanka na shirya tsaf nasa kayana sannan na kama hanyar zuwa gidansu gimbiyata husna.
Na dade ina tafiya da kafafuna sannan na samu na karasa kofar gidan ai kuwa tun kafin na tsaya naga itama ta fito kamar tasan cewa na iso.
Da tattausan murmushinta ta tareni sannan taimin umarni damu karasa cikin gidan nasu..
Banyi mata musuba ta shige gaba na bita a baya har muka karasa cikin farfajiyar gidan, cikin gidan an kawatashi da kayayyaki na alatu da jin dadin rayuwa ga shuke shuke masu matukar kyau da daukar hankali furenninsu sai kamshi suke.
Karkashin wata bishiyar zaitun nan ne inda husna ta tanada mana ma'ana nanne inda za muyi shirar da ita a wannan yammacin...
Bayan ta nunamin wata kujerar roba da take girke a gun su biyu suna fuskantar juna sai kuma dan wani tebir da aka ajiye a tsakiyar kujerun ma'ana sune suka raba tsakanin kujerun...
Ban jira komaiba na karasa na zauna itama tazo ta zauna a daya kujerar muka fuskanci juna nida ita babu wanda yace da wani kala, saida muka dauki lokaci muna kallon kallo nida ita sannan husnan ta katse shirun namu da murmushinta mai daukar hankali sannan ta fara yimin magana da yar siririyar muryarta mai kamar ana busa sarewa tace dani...
Yaya Abdul ashe dama zaka zo?
Murmushi kawai nayi sannan na dubeta har cikin idanunta nace haba husna menene zai hanani zuwa gareki in har ina raye?
Gaskiya naji dadin zuwanka sosai dan wallahi jiya kusan kasa bacci nayi saboda kewa da kuma tunaninka harma so nake gari yai saurin wayewa na kiraka na danji muryarka sai kuma na tuna ashe baka da waya husna ta sake cewa dani tana wasa da yatsun hannunta...
Murmushi kawai nayi sannan nace karki damu husna ai gashi nazo gareki dan kuwa nima kaina saida tunaninki ya dinga kaiwa da komowa a cikin zuciya naji babu wacce nake kaunar sake gani kamar ke kunnuwana kuma muryarki kawai suke bukatar suji nima nai mata wannan furucin...
Na gode kwarai yaya Abdul dina gashi kuma mun tsaya sai zuba muke ko ruwan sha ban kawo maka ba na barka da yunwa gamida kishirwa husna ta fada tana kokarin mikewa tsaye daga kan kujerar da take...
Husna kenan aini babu wata yunwar da nakeji a halin yanzu tunda ina tare dake haka kuma zan iya shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da naci ko kuma nasha wani abuba idan har kina kusana dan kuwa sautin muryarki shi kadai yakan gusarmin da yunwar da nakeji haka kuma ganin wannan kyakkyawar fuskar taki mai annuri yakan kawarmin da kishirwar da nakeji nace da ita...
Lumshe idanunta kawai tayi sannan ta bude ta dubeni tace yaya abdul kalamanka suna matukar birgeni ina jin dadinsu sosai da sosai dan haka jirani ina zuwa tana maganar ta kada kanta ta nufi cikin gidan nasu..
Nai shiru ina tunanin wannan hali na mutuncin da husna taimin na dubi girman gidan gamida tsarin da yake dashi na kuma tuna yadda tsarin namu gidan yake na kasa ne haka kuma ya tsufa dan kujejjen rufinsa duk yayi baki saboda yawan shekarunda ya shafe, muna matukar shan wahala musamman idan lokacin damuna ne dan kuwa idan har ana ruwa to kusan a tsaye muke kwana saboda fashewar da rufin dakunan gidan namu ke dashi na girgiza kai na tuno cewa wai idan zanyi aure dole sai dai a bani daya daga cikin tsofin dakunan dake cikin gidan na tare da amaryar tawa...
Anya kuwa husna zata amince ita da take zaune a cikin wannan katafaren gidan?
Na tambayi kaina lokaci guda ina tunanin girman matsayinta.
Mezai hana ta amince idan har tana kaunar taka wata zuciyar ta fadamin...
Gaskiya akwai abin mamaki idan har husna zata iya zama a gidanmu dan kuwa ko kusa baiyi tsari da irin gidajen da yayan manyan masu kudi suke zaman aure a cikiba sauda dama nakanga babu wani da yake auren yar gidan mai kudi sai yayan masu kudi ko kuma yayan sarakuna da kuma manyan yan siyasa..
Haka kuma sau tari yayan talakawa sunfi auran ruwansu ma'ana yan uwansu talakawa..
Ban gama tunaninda nakeba sanadin zazzakar muryar husna da takemin magana..
Firgigit nai saurin daga kaina na dubeta sannan wani dan fatalwan murmushi ya subuce daga fatar bakina...
Yaya Abdul dina tunanin me kake haka? Husna ta tambayeni tana kallona...
Tunani kuma husna? Na maida mata da tambayar da tayi a gareni...
Eh tunani mana abdul, dan Allah tunanin me kake? Ta sake tambayata.
Husna tunanin yadda rayuwarmu zata kasance gaba nakeyi musamman idan na tuna yadda zamu rabu dake nai mata karya a karo na farko, wanda ni kaina nasan ta gane hakan.
Kuramin ido tayi kamar wacce zata gano abinda ke damuna sai kuma lokaci guda tayi murmushi ta zauna a kujerar da ta tashi dazu.
Ta dade idanunta suna kaina ni kuma na kasa cewa kala tun daga maganar da na fada mata tun dazu, yaya Abdul waye ya fada maka zamu rabu haka kuma wa zai rabamu da kai? Lokaci guda ta jeromin wadannan tambayoyin nata har guda biyu...
Husna a hakikanin gaskiya ke baki kasance daga cikin irin matannan da suka taso cikin wahala da talauciba haka kuma ina tunanin rana a tsaka bazaki iya samun kanki a cikin irin wannan halin ki jure ba na sake cewa da ita..
Eh abdul maganar da ka fada ta farko gaskiya ne cewar na taso cikin jin dadi to amma waye ya fada maka bazan iya jure zaman talauci ba? Husna ta sake tambayata...
A gaskiya husna ina tunanin bazaki iya zama a gidan mu ba dan kuwa gaskiya a yadda naga gidanku yadda kika taso cikin jin dadi bani tunanin zaki iya zama a gidanmu mu talakawa..
Karka damu abdul in dai nice bana tunanin akwai yanayin da bazan iya jurewa ba indai akanka ne dan haka rike wannan ta mikomin wani abu a cikin leda..
Nai sauri na dubeta nace husna menene a ciki haka da kikamin kyautarsa?
Comments
Post a Comment