Abubuwa guda hudu wanda ya kamata duk mai cin naman kaji ya sani
Kaji suna daga cikin halittun da ake ci mafi daraja daga cikin jinsin tsuntsayen da muke amfani dasu ayau da kullum saboda Dadin namansu da kuma amfanin da akeyi da kwansu saboda Dadi da kuma mahimmancin sinadaransu a jikinmu.
Kaji sun kasu izuwa kashi biyu anan Najeriya Wato kajin turawa (exotic chickens) da kuma kajin gida ko na hausa (indigenous chicken). Dukannin wadannan kaji ana Nijeriya ana cin namansu da kuma kwansu. Saidai kuma wani abu Wanda baza'a iya tantance dalilin saba shine yadda mutane suka dauki naman kajin turawa da kuma kwansu da matukar mahimmanci wajen ci sama da namu na gida domin kuwa kusan duk Inda mutum zaije domin cin naman kaji zaiyi wuya ace naman kajin gida ne a wajen.
To koma dai menene dalili sashen kimiya na duniyar labari ya zakulo muku mahimmancin da cin naman kajin Hausa ko gida keda shi a lafiyarmu. Abubuwan da kajin gida keda su sune kamar haka:
Karanci guba
Kajin gida ko kajin Hausa suna da karancin guba a nama sakamakon karancin yin amfani da sinadaran magunguna da masu kiwonsu ke amfani dasu a yayin kiwonsu. Domin su kajin gida anyi ittifakin suna da garkuwar jiki sama dana turawa Wanda sai an tagaza musu da sinadaran girma Dana karfafa jiki haka kuma a kowane lokaci suna cikin tsarin bayar da magungunan rigakafi har sukai matakin sayarwa a kasuwa, da wadannan sinadaran mu kuma muke saya muci cikin halin rashin tabbas din maganin ya sake su ko bai sake suba a yayin da wasu sinadaran maganin sukewa naman kajin kamun kankamo. Cin naman kajin Hausa yana da matukar amfani domin matukar mutum nason yaci naman kaji Wanda bazai cutar dashi ba to ya samesu ya saya domin gujewa fadawa matsalar cututtukan zamani irinsu cutar daji,cutar hanta ko cutar koda dadai sauransu.
2. Yawan sinadarin vitamin D
An tabbatar da cewa Kajin gida ko Hausa suna dauke da sinadarin vitamin D mai yawan gaske, wannan sinadari Nada matukar mahimmanci a jikin Dan Adam tare da inganta lafiyarsa.
3. Karancin kitse
Kajin gida ko na Hausa suna da karancin kitse akan na turawa kona gidan gona,yawan cin naman kaza mai kitse zai iya kawo damuwa ga masu hawan jini da ciwon suga,saboda babu abin da kitse zaiyi ga mutane masu cutar da basa bukatarshi face kara masifa, bayama ace sun kasance ma'abota cin naman kazar bature ne. Anan ga mafita duk mutumin dake da da wata matsala akan cin nama mai kitse to ya nemi na kajin gida domin suna da karancinsa a jiki.
4. Matukar dandano
Wannan basai anyi jawabi mai tsayi ba akan dandanon da naman kajin gida keda shi, idan har mutum ya taba cin naman kazar turawa to ya sani naman bashi da dandano saboda duk abincin da ake basu ya samu ne daga abinci mai dauke da sinadarai masu hura jiki ne kawai bawai kara dandano ba.
Ga mutane masu sha'awar kiwon kajin gida a zamanance sukasance masu bibiyarmu a koda yaushe.
Comments
Post a Comment