Abubuwan da baza a manta dasu ba.
Shekarar dubu biyu da ashirin tazo da wasu abubuwa wanda zaiyi wuya a manta dasu koda a tarihi ne domin abubuwa da dama sun faru wanda baima kamata a manta dasu ba.
Yanzu zamu lissafa wasu abubuwa wanda suka faru a wannan shekarar ta dubu biyu da ashirin..
BATANCI GA ANNABI
Cikin shekarar dubu biyu da ashirin aka samu wata jarida data samu goyon baya daga shugaban kasar faransa harma sukai batanci ga shugaban mu annabinmu mai daraja.
Hakika ciwon wannan abin zai jima a zuciyarki.
CORONAVIRUS
Itama wannan baza mu manta ta ba saboda annoba ce wacce aka jima ba a samu irinta ba domin da tazo ta hana dukkan abubuwa dake tafiya a kasa kama da harkar karatu tafiye tafiye da sauran al'amura na rayuwa hakika cutar corona ta shiga tarihin da bazata mantu ba.
HANA SALLAH KO KUMA AIKIN HAJJI
Nidai iya sanina inba a tarihi ba ban taba jin a shekarar da aka hana sallah ba cikin masallatai harda aikin hajji sai a wannan shekarar ta dubu biyu da ashirin dan haka zaiyi wuya tarihi ya manta da shekarar.
MUTUWAR MANYAN MUTANE
Cikin shekarar dubu biyu da ashirin an samu mace mace na manyan mutane wanda aka jima ba ai irinsu ba koda a tarihi domin mutane masu girma sun mutu.
SACE DALIBAN MAKARANTAR KANKARA
hakika sace daliban makarantar kankara zai zamo cikin ababan bada tarihi na shekarar dubu biyu da ashirin.
TAKADDAMAR AMERICA DA IRAN
An jima ana takaddama tsakanin kasashen biyu a wannan shekarar dan haka shima zai zamto abin bada tarihi na shekarar dubu biyu da ashirin.
CIRE SARKI SUNUSI NA BIYU..
A wannna shekarar aka cire sarki sunusi lamido sunusi akan karagar mulki wanda hakan ya kawo cece kuce da yawa harma ya shiga cikin manyan abubuwan da baza a manta dasu ba a shekarar.
ENDSARS
wata zanga zanga ce da tazo da wani salo na ban mamaki domin anyita ne da manufofi da dama sannna ta jawo asara mai tarin yawa a kasar nigeria. Zanga zanga ce da wata mace ta jagoranta.
KISAN MANOMA 43 A ZABARMARI..
Kisan manoman ya kafa tarihi wanda bazai mantu ba kuma shima ya zo ne cikin shekarar dubu biyu da ashirin.
WANI PHOTO DA RAHMA SADAU TAYI.
Fitar da photon da yar wasan hausan tayi baiyiwa musulmai dadi ba domin maganganun da da akai cikin photon baiyiwa mutane da dama dadi ba.
Comments
Post a Comment