Wata dama tazo ga dukkan wanda yasan bai hade layikan wayarsa da NIN number ba
Biyo bayan yawan korafe korafe da mutane da dama ke yi ganin cewa basu samu damar hada layukansu da NIN number su ba yasa hukumar dake kula da bangaren yin wannan aikin da kuma masu bangaren nin number suka sake fitar da ranar da za a sake rufe wannan register, ina nufin an kara wasu kwanakin sabanin 19 ga wannan watan na janairu da aka sanar a matsayin ranar da za a dakatar da yin register zuwa ranar tara ga wata mai kamawa na February.
Tun jimawa aketa sanar ga dukkan ilahirin dan nigeria dake da layin waya cewar yai maza ya mallaki katin dan kasa sannan an fitar da hanyar da zai hada NIN number tasa da dukkan layin wayarsa saboda tsaro wanda yai karanci a kasa, wanda hakan zai bada damar samun tsaro mai inganci domin kowa bayaninsa zai zama ana gani hakan zai bada damar dakile duk wata hanya da ake bi wajen yin ta'addanci da sace sace a kasa.
Hakika wannan dokace da mafiya yawan mutane suka karbeta hannu bibbiyu saboda ingancinta. Dan haka ake sanar da duk wani da yasan bai hada layin wayarsa da NIN ba da yayi sauri ya hada kafin zuwan ranar tara ga watan February na wannan shekarar.
Karin haske
Sannan ana kira da mutane su guji yadda wasu suna karbar NIN number su domin su hada da layin wayarsu domin hakan kuskure ne babba domin idan ka bada NIN number ka wani yai register da ita to duk lokacinda ya aikata wani laifi kai za a kama dan haka ake kira ga mutane da su guji aikata hakan.
Sannan ku gane wannan NIN number din tanada matukar amfani kuma tana bukatar tsaro da kulawa ga duk wanda ya mallaketa domin tana dauke da bayanan mutum tun daga farko har karshe.
Comments
Post a Comment