Yadda giwaye ke jana'izar yan uwansu tare da zaman makoki ( tarihin halittu)
Anan zamuyi dubane dangane da yadda dabbobin daji keyi idan suka rasa nasu a sanadiyar farauta ko rashin lafiya.
Alokuta da dama zaki idan zaiyi farauta yana shigane cikin dandazon dabbobi a daji ya kama yaci harya bari, a yayin da saura kuma suke tserewa subar gawar dan uwansu anan idan yaci koshi ya tafi yabar sauran ya rube ba tare da sauran sun waiwayi gawarba Dan daukan wani mataki kamar jana'iza ko sutura ko kuma zaman makoki, abin tambayar anan shine irin wadannan dabbobi bayan tsoran da suke dashi na kada a kamasu a cinye shin sunajin wani abu kuwa mai kama da alhini ko damuwa na rashin wannan Dan uwa nasu ko kuma shikenan ya zama tarihi?
Anan an samu wasu dabbobi kalilan da suke nuna alhini na rashin Dan uwansu da sukayi, abin mamaki anan shine giwaye ma sun fado cikin jerin dabbobin dake zaman makoki a bisa mutuwar daya daga cikinsu harma suna gwada yi masa sutura ko jana'iza a matsayin gawa.
Masu Bincikice da dama sun dade suna zargin giwayen da yiwa yan uwansu jana'iza bayan sun mutu duk kuwa da cewa basu fitar da wata kwakwkwarar hujja ba ta bidiyo dake nuni da hakan. Gaskiyar maganar cewa giwaye nayiwa gawar yan uwansu jana'iza bata fito fili bane karara watakila kodan su ba halittu bane Wanda mutane ke sha'awar dauka a bidiyo sosai, duk da an samu bayanai da suke cewa masu farauta sun sha buya cikin duhuwa suna ganin yadda giwaye ke rufe gawar yan uwansu da ganyayyaki.
Dadi da kari masu bincike sunyi karin bayani cewa sun sha cin karo da kaburburan (makwantai,kushewa) giwaye a yayin da suke bincike, domin an gano dangin giwaye suna da dabi'ar Tattara gawawwakin 'yan uwansu waje guda cikin rami daga bisani su saka musu yayi a kai su rufe su. Haka kuma kamar yadda yan Adam kan nuna damuwa ko alhini a matsayin zaman makoki ahlin giwaye ma suna zaman makoki ta hanyar nuna kasalar jiki tare da canjawar yanayinsu a duk lokacin da suka rasa nasu, suna nuna darajantawa ga ran Dan uwansu da suka rasa cikin girmamawa.
Wannan al'amari na yadda giwaye ke nuna kulawa akan yan uwansu ya isa a kirashi da abin al'ajabi ko kuma mu kirashi da baiwa babba.
Comments
Post a Comment