Yar Nijar
Tai saurin tashi tsaye a firgice idanunta a zazzare saboda tsananin firgita..
"Me nake gani haka a hannunka abdul?" ta fada da alamun mamaki karara a fuskarta
Me idanunki suka fada miki na fada ina zazzare idanu ko kadan babu alamar wasa a tattare da fuskar tawa..
"kamar wuka nake gani a hannunka abdul" ta kuma fada har yanzu bata gaskata abinda idanunta suke gane mataba
Eh wukace haka kuma ba kowa take jiran tasha jininsaba sama dake dan ko tantama banayi yau zaki bakunci lahira dukiyarki da kika kashe mijinki kika gada nima nine zanci gaba da shan sha'anina da ita na fada ina jujjuya sabuwar wukar da take hannuna ina duban bangaren da zan fara luma mata wukar a jikinta.
Ita kuma ta zuramin idanu tsananin mamaki da kaduwa ya hanata kokarin yin kome ta kuma bude bakinta da kyar ta fara magana bakinta yana karkawarwa tace..
" yanzu abdul me nayi maka zaka kasheni ko kuma wannan shine SON da kace kanamin haka kuma shine kaunar taka da kake ikirarin sanar dani kana cewa kai mai kauna ne a gareni... Ta kasa karasa maganar da take kokarin yi sanadin zazzafan tunanin daya fusgi zuciyarta farkon haduwarta dani...
Dan koni da nake tsaye da wuka a hannuna saida tunanina ya koma baya farkon haduwata da ita a kasar NIGER
Farkon faruwar lamarin
kamar yadda mutane suka bambanta, hakama ra'ayin rayuwarsu ya bambanta.
Zamantakewar al'adu mu'amala ilimi da sana'a da dai sauransu, shakka babu na wasu yasha bambam dana wasu..
Wasu a rayuwarsu sunfi so da kaunar jin dadi da daular duniya da dukiya ko kuma mulki ko kusa basu son su sha wahala su saidai a barsu kawai babu aikin fari balle na baki, kullum sai dai su wanke goma su tsoma biyar..
Duniya kenan mai al'amura da yawa, a lokacin da wadansu kejin dadi wasu kuma al'amura sun dagule musu suna fama da wahalar rayuwa da tsananin talauci da sauransu..
Daki daki abubuwan suke tafiya ma'ana daya bayan daya ko kuma nace sahu sahu, tun daga manyan kasashe zuwa birane da kuma kauyuka kai harma da sauran kebantattun gurare wanda bil'adama suke zama dansu rayu..
Na daga kaina sama, sararin samaniyar yayi bakikkirin yayinda aka ci gaba da ruguntsuma tsawa nan da can a cikin babban birnin na zinder dake kasar Niger...
Tun dazu nake tsaye a bakin titin ina jira da sauraron zuwanta
Nakai kallona ga fuskar agogon dake hannuna karfe biyar da rabi na yamma, sannan na kuma maida dubana kan titin motoci gamida babura sai wucewa suke a guje kowa yana kokarin ya isa gida kafin tasowar hadarin babu wani daya damu da wani hankulan kowa ya karkata ga hadarin da yake kokarin tasowa...
Na sake gyara tsayuwa a gefen titin ina tunanin dalilin dayasa har yanzu liliane bata karaso ba duk dama munyi waya da ita tace tana hanya..
"Anya kuwa zata zo abdul ba tsaraka kawai tayiba" naji zuciyata ta fada..
Nai saurin kawar da wannan tunanin da nake daga zuciyata dan ba abune mai iyuwaba ta gaiyatoni bikinta ita da mijinta MUNNIR MIMO na taso tun daga nigeria nazo niger amma kuma taki zuwa nai shiru sanadin iska mai karfin da na faraji tana busawa hakan shine ya bani tabbacin hadirin ne ya fara tasowa...
Na sake duban agogon a karo na barkatai karfe shida daidai na yamma kuma ga har yanzu ba liliane ba alamarta sai yanzu na fara gaskata maganar da zuciyata ta fadamin da farko cewar tsarani kawai liliane tayi ni kuma dan iyayi da son yawo da kuma neman suna na taso tun daga nigeria nazo niger, tab! amma idan hakane to a gaskiya ko kusa bata kyautaminba dan zan iya cewa ma batamin adalciba ko kadan nai shiru sanadin yayyafar da naji ta fara sakkowa a bisa kaina waiyo ina zansa rayuwata wai yau nine a birnin zinder kasar Nijar
Zanci gaba idan kuna biye dani a wannan website din dan haka kuyi following dinmu.
Comments
Post a Comment