Min menu

Pages

AN GANO WANI HATSABIBIN MACIJI MAI FUKA-FUKAI A KASAR NAMIBIA

 AN GANO WANI HATSABIBIN MACIJI MAI FUKA-FUKAI A KASAR NAMIBIA


Cikin shirinmu na zagaya Duniya da kuma tarihin duniya da halittun cikinta yau munzo muku da labarin wani hatsabibin maciji da yake da fuka fiki kamar tsuntsu yana tashi sama.

Ku biyo mu cikin labarin

An gano Wani Maciji mai fuka-fukai dake tashi sama a kasar Nimibia, macijin na daga cikin irin jinsin mahaukatan macizan dake da tawaya (Gargantuan sarpent), anyi ittifakin jinsin irin wannan maciji nada daga cikin irin macizai masu tashi da ake bada labarinsu masu alaka da jegare (dragon).


An bayyana wannan maciji da siffa mai kalar ruwan dorawa da kuma ruwan kasa haka kuma yana da dan digo mai haske ko baki a jikinsa.


Bayanai sun bayyana cewa macijin nada tsawon daya kai kafa 9-25 haka kuma wannan maciji na iya sajewa da duk inda ya shiga.



Macijin Gargantuan yana da bakin siffofi Wanda ba safai akan sami macizai da suba ko kuma ma babu saidai idan ko a shidin kawai, macijin nada siffofi kamar fuka- fukai irin na jemage mai dan gashi-gashi.


 Wanda yake  tashi dasu a cikin iska, fuka-fukan idan suka bude sunkai kafa 30, yana da wuya Wanda cikin sauki zai iya kumburashi koya iya motse shi ta hanya guntsar iska tare da furzarwa.


An ce macijin na wata kara mai matukar tsoratarwa, yana kuma fitar da wani irin wari mai kama dana kwalta, domin tashi cikin iska yana buga kansa kasa da karfi akan tudu.


Wannan maciji an same shine a yankin Karas dake kasar Nimibia, wani mutum mai suna Michael Esterhuise yace yaga wannan maciji a shekarar 1942 a gonar tumakinsa Wanda keda nisan kilomita 60 daga yammacin garin Keetmanshoop, yace sau biyu yana ganin katon macijin a lokacin dayake buga kansa akan tudu zai tashi sama.



A bayan shekara 1950 a wata gona dake kusa da Goageb, dandazon wasu manoma da mishinari sun sami gawar tumaki 7 wanda suka mutu a sanadiyar cizo da wata halitta mai kama da maciji tayi musu, cizon yayi alama ta kananan hudoji biyu, amma bayan samun gawar tumakin babu wanda ya fahimci a wajen akwai wani abu mai kama da toka, sai daga bayan kuma aka gano burbudin toka-toka a jikin gashin fatar tumakin.


An sake samun labarin ganin wannan maciji a shekarar 1978, inda wani manomi dan asalin kasar faransa yana kora garken dabbobinsa a yankin Karas a kasar Nimibia. 


Yace yana cikin tafiya cikin garken shanunsa kawai saiya hangi wani abu mai dan haske, saida ya lura sosai sai yaga abin kai tsaye wajen da yake tsaye da dabbobinsa yakeyi. 


Bayan wani dan lokaci yaji saukar wani abu a cikin shanunsa a lokaci guda kuma saniyarsa guda tayi wani irin kuka, yana dubawa yace sai yayi arba da maciji ne mai fuka-fukai ya kafa bakinsa a jikin saniyar, cikin azama ya koma da baya yayi bayanin abin dake faruwa a gonarsa ga yan sanda.  

Comments