Min menu

Pages

AN KONA MASALLACI A GARIN BILLIRI JIHAR GOMBE


AN KONA MASALLACI A GARIN BILLIRI JIHAR GOMBE

Rikicin Sarauta a tsakanin kabilar Tangale daje garin Billiri jihar Gomhe ya fara juyewa zuwa rikicin addini

Kwanakin baya Sarkin Tangale wanda ba Musulmi ba ya mutu, yanzu kuma wanda Gwamnatin jihar Gombe ta zaba ya maye gurbinsa Musulmi ne kasancewar ya gaji Sarautar, sai wadanda ba Musulmi ba suka ki amincewa duk da kabilarsu daya

Rikicin nasu na Sarauta yana neman sauya salo zuwa rikicin addini, domin har an kona Masallaci a garin Billiri a yau

Menene laifin Masallaci akan rikicin Sarauta da za'a konashi?
Hakika wadanda suka kona Masallacin ba su nemi zaman lafiya ba, ya kamata hukuma ta zakulosu don su fuskanci hukunci

Muna fatan Allah Ya kawo zaman lafiya a garin Billiri dama kasa baki daya.


 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments