Min menu

Pages

An YiWa Ƙananan Yara Shida Kisan-gilla A Rugar Fulani Makiyaya A Anambra


 Yadda Aka YiWa Ƙananan Yara Shida Kisan-gilla A Rugar Fulani Makiyaya A Anambra 


Fulani makiyaya da ke zaune a wata ruga da ke ƙauyen Oba cikin Ƙaramar Hukumar Idemili ta Jihar Anambra, sun zargi ’yan tada zaune tsayen IPOB da kashe masu ƙananan yara shida ‘yan ƙasa da shekara 10.


Sai dai kuma Fulanin sun shaida wa wakilin Blue Print cewa ba za su ɗauki fansa ba, domin su na jiran su ga abin da hukuma za ta yi domin bi masu haƙƙin su da ita gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta yi.


Wannan hari da kisan da aka yi wa ƙananan yaran ya faru ne a ranar Talata, amma dai abin bai bayyana ba sai a ranar Alhamis.


Munanan hotunan da ke hannun Blue Print sun nuna irin kisan wulaƙancin da aka yi wa ƙananan yaran, wadanda aka sassara da adduna. Wani da bai wuce shekara daya ba ma kone shi da wuta aka yi.


Cikin hotunan akwai na gidajen da aka banka wa wuta. Sannan kuma alamomi sun nuna an afka wa kananan yaran an kashe su ne, saboda lokacin da masu ta’addancin su ka dira rugar, ba su samu manya a wurin ba, sai su ka afka wa kananan yara da sara, har su ka kashe su.


Sannan kuma Blue Print ta samu hotunan ƙananan yara a cikin likafani, kafin a kai ga rufe su cikin kaburbura.


Wannan mummunan hari ya sa mazauna rugar duk sun rasa muhallin su.


‘Gudun Hijira A Barikin Sojojin Onitsha’


Wadanda su ka tsira da rayukan su dai a yanzu haka su na zaman gudun hijira ne a barikin soja da ke Onitsha. Wani da ke zaune a barikin mai suna Dogo Isa da majiyar cikin sojoji da kuma Mahmud Imam sun tabbatar wa Blue Print cewa su na can a barirkin na sojojin Anacha.


Dukkan kananan yaran dai an rufe su ne a cikin makabartar barikin sojojin Onitsha .


Amma Kakakin ’Yan Sandan Anambra, Haruna Mohammed ya bayyana cewa ba shi da labarin kisan.


Sunayen Wadanda Aka Yi Wa Kisan-gillar Su Ne:


1. Nasiru Laminu, dan shekara biyu;


2. Sirajo Ali, dan shakara biyu;


3. Zainabu Mutmeru, dan sharara hudu;


4. Aminu, mai shekara biyu;


5. Mairo, mai shekara shida; na cikon


6. Maryam, ’yar shekara daya da haihuwa.


Dogo Isa wanda ya shaida wa wakilin mu sunayen kananan yaran da aka kashe, ya ce ba a kashe masu saniya ko daya ba.


“Ba a kashe mana shanu ko daya ba, saboda a kollacin an tafi da dukkan shanu korama domin su sha ruwa.


“Shekara ta 43 a Jihar Anambra. Amma a ranar Litinin sai wani ya kira ni ya ce mani da ni da iyali na duk mu kwashe komai na mu daga jihar, mu fice.


“Mutumin ce min ya yi na kwashe kayana da dukiya ta da iyali na duk na koma Arewa, domin daga ranar ba su bukatar ganin mu a kasar Inyamurai.


“Su ka ce min sun ba ni kwana daya kadai na kwashe kaya na bar jihar. Amma washe gari ranar Talata sai aka kira ni wajen karfe biyar na yamma, aka ce na je gida. Ina zuwa sai na tarar da gwawarwakin yaran mu kanana shida, kuma an banka wa gidajen mu wuta. Dalilin yin gudun hijirar mu a barikin soja kenan.”


Isa ya ce ana rade-radin wai Fulani na gangamin zuwa yin ramuwar-gayya. To amma wannan ba gaskiya ba ne. Na dai roki sojoji su taimaka su gano mutumin da ya kira ni da wata lambar waya domin a kama shi.


Ya ce jama’a da dama wadanda su ke zaman lafiya da zaman amana a cikin kabilun Igbo da ya ke zaune tare da shi, su na ta kiran sa domin yi masa jaje da jimami, ta’aziyya da lallami.


A karshe ya ce idan aka kamo wanda ya kira shi da waya ya ba shi wa’adin ficewa cikin kwana daya, to ta haka ne za a iya gano sauran wadanda su ka kai harin kisan-gillar har suka kashe kananan yara shida.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments