CBN YA UMARCI BANKUNA DA KARBAR WADANNAN TAKARDU WAJEN BADA KUDADE
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci dukkannin bankunan kasuwanci dake harkokin kudade a Najeriya da suna karbar duk wata takardar sheda ta tafiye-tafiye, ko duk wata takarda dake nuni da shedar gudun shijira. Bayanin yayi nuni ga dukkanin wuraren da ake kasuwancin kudade (Bankuna)dasu karbi takardun shedar tafiye-tafiye kona gudun hijira matukar takardun za'a iya daukar bayanansu a na'ura (photocopy da scanning), wajen karbar kudade ko saka kudade a asusun ajiya.
Wannan umarnin ya fito ne ta baki Dr.kevin Amugo, daraktan fannin kudade da tsare-tsare na CBN , yayi wannan sanarwa a ranar laraba, a sanarwar taxa yace ya ce bankunan su rika amfani da halatattun takardun tafiye-tafiye wajen baiwa mutane damar cire kudade. Dr. Kevin ya kuma roki bankunan dasu kara himma ta fuskar abin daya shafi cire kudade da mutane keyi a asusan ajiyar kudadensu, ko domin a samu karancin amfani da haramtatun kudade da kuma munanan aiyuka na ta'addanci ta fuskar bankuna.
Comments
Post a Comment