Min menu

Pages

Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani Gwamnan Apc

 Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani Gwamnan Apc



Alkalin wata kotu a jihar imo Fred Njemenze ya bada umarnin tatttare duk wata kadara da tsohon gwamnan jahar ya mallaka Wanda ba halattacciya ba.

Alkalin kotun ya bada umarnin kwace kadarorin tsohon gwamnan jahar ta imo wato Rochas Okorocha Wanda bana halas ba wanda ya mallaka a lokacin mulkinsa daga 2011 zuwa 2019.

Alkalin ya bada umarnin ne kamar yadda babban lauyan Najeriya  mai suna Louis Alozie ya bukata a madadin gwamnatin jahar.

An lissafo wasu kadarori da aka ambata na tsohon gwamnan ne wanda ba halattattu ba da suka hada da Jami'ar Eastern palm dake Ogboko, kwatas din malaman IBC Wanda aka ce gidauniyar Rochas ta samu ba bisa ka'ida ba, hotel na Royal spring palm da kwatas majistare da sauransu, Legit ta ruwaito.

Rochas Okorocha tsohon gwamnan jahar Imo ne kuma mai mallakin Gidauniyar Rochas, shine mutumin dake gina makarantu na musamman kyauta a dukkannin fadin Najeriya tare da bada scholarship kyauta ga 'ya'yan masu karamin karfi. Rochas yayi takararsa ta farko a karkashin jam'iyar All progressive Grand Alliance (APGA), sannan yayi takara ta biyu karkashin jam'iyar All progressive Congress (APC).

Comments