Kudaden kasashe goma da sukafi daraja a Africa kasar farko data takwas sunfi bada mamaki
Abune bayyananne da kusan mutane da dama ke ganin cewa kalar kudin da kowace kasa ke amfani dashi yana nufin cewa darajarsa nada alaka da girman tattalin arziki da kasar ke dashi tare kuma da karfin da kasar ke dashi wajen yadda al'ummarta ke iya rayuwa mai kyau wajen morewa.
Akwai sabani tare da rudu mai yawa akan maganar dake cewa sanannu kuma manyan kasashe sune suke da kudade masu matukar daraja, wannan zance gaba daya ba gaskiya bane idan har mukayi la'akari da darajar da wasu kudaden kasashen Africa kedasu.
Dole za'a sami ra'ayoyi mabam-bamta dangane da ta yadda wata kasar ta zama ta farko kuma mai karfin tattalin arziki.
Idan har kasa ya kasance tana amfani da kudin da baiyi daidai da tattalin arzikin taba to dolene sauran kasashe suzo su kereta su sha gabanta.
Mutane da dama zasu iyayin tunani ko imanin kasar Najeriya da Africa ta kudu kudin su nada daraja, sai dai ina abin ba haka yake ba.
Anan muna da kasashen Africa goma Wanda kudadensu keda matukar daraja daga na goma har zuwa na daya.
10)Egyptian pound(E£)
Wannan shine sunan kudin da ake amfani dashi a kasar masar (misra), Egyptian pound mai darajar E£ 16.30 dai-dai yake da 1USD (Dollar daya ta America). Kudin kasar masar yazo cikin kudade goma mafiya daraja a Africa domin ya sami daraja ne bayan da kasar ta rage kudaden haraji da take karba a wajen yan kasuwa na cikin gida dana waje.
9) Eritrean Nakfa (NKF)
Wannan shine kudin da mutanen kasar Eritrea ke amfani dashi ana kiransa da NAKFA. Dala 1 daidai take da NAKFA 15.00. Nakfa kudi ne Wanda keda daraja kuma darajarsa bata fiya saukaba sakamakon gwamnatin Kasar Eritrea bata caccanja fasalin kudinta, sannan sun zabi yin amfani da tabbatacciya hanyar canzar da kudadensu guda daya.
8) South African Rand
A yanzu haka dala daya daidai take da RAND 14.87. Wani zai iya tunanin kudin south Africa nada matukar daraja, to ka sani tun shekaru da dama darajar kudin south Africa keta sauka kasa.
Zan so mai karatu ya kwana da sanin cewa Namibian dollar, Lesotho loti da Swazi lilangeni suma suna jone ne da kudin Rand, hakan yana nufin darajarsu suma ta ta'allaka da darajar da south African Randa keda ita.
7) Saychellois Rupee
Rupee shine sunan kudin da saychelles ke amfani dashi shine na bakwai a jerin kudade goma mafiya daraja a Africa. A yanzu haka SR 13.64 daidai yake da darajar dala daya, sakamakon tsaurin da suke dashi da kuma manufofi kan dukiya a kasar. kudin kasar ya kara daraja a baki dayan Nahiyar Africa.
Hakazalika, saboda kasuwancin abubuwan dake bunkasa tattalin arziki tare da fitar da kayayyakin kasar Wanda suka wajen inganta kananun masana'antu tare da daukan noma da mahimmanci wajen canja fasalinsa hakan ya sake karawa kudin kasar daraja.
6) Zambian kwacha (ZK)
A yanzu haka dala daya daidai take da darajar ZK 13.14, Zambian kwacha yana da daraja mai karfi saboda Zambia itace kasa tilo dake fitar da adadin copper mai yawa da kasar ke samarwa zuwa kasashen duniya.
Copper ma'adani ne dake da matukar daraja Wanda ake fitar dashi zuwa kasashen ketare, wannan na nufin matukar ma'adanin da kasa ke fitarwa nada matukar daraja to hakama kudin kasar zaiyi daraja. Wannan ne ya saka kudin ZK yake da daraja sakamakon darajar cooper a kasuwannin duniya.
5) Botswana Pula
Dala daya daidai take da darajar P 10.90. Botswana pula yayi daraja ne saboda daidaitacciyar dimokradiya da kasar ke a kai tare da kakkarfan tattalin arziki.
A matsayin ta biyar a darajar kudi cikin kasashen Africa har yanzu darajar kudinta kara hawa take, saboda da safarar kayayyaki da suke zuwa ma'ajin Johannesburg dake Africa ta kudu domin musaya.
Idan ba'a manta ba a shekarar 1976 darajar musaya da akeyi tsakanin Botswana da Africa ta kudu saida yakai darajar Botswana pula takai ta Rand.
4) Moroccan Dirham
Dirhamin marocco MAD 9.89 daidai yake da Darajar Dala daya. Bayani ya tabbatar da cewa Moroccan Dirham shine madubin dubawa Wanda ke shiga tsakanin masu musaya a yamma da sahara. Wannan shine ya sanya kudin zama mai matukar daraja, Darajar da saida ya zama na hudu a jerin kudaden Africa goma mafiya daraja.
3) Ghanian Cedi
Dala daya daidai take da darajar Ganian Cedi 5.49, a tsawon lokaci cikin shekaru da dama darajar kudin kasar Ghana tabarbarewa yayi tayi har sai bayan da aka maye wajensa da Cedi a shekarar 2007 aka sami daidaituwar tsarin.
Tun daga wannan lokaci kudin Ghana yayi ta daraja ta yadda kasar tayi taci gaba ta fuskar kudade, Wanda a yanzu sune akan gaba wajen darajar kudi a kasashen yammacin Africa. Dadi da kari shirye-shiryensu na kashe kudade wajen Samar da ayyukan yi zai sake basu dama su cigaba da zama na gaba wajen darajar kudi a Africa.
2) Tunisian Dinar (DT)
Tunisian Dinar yana da darajar DT 2.87 a dala daya. Bayan sun canja kudin su tun a shekarar 1960 daga Wanda turawan mulkin mallaka na faransa suka bar musu. Sun samar da Tunusian Dinar, yanzu haka sunyi shekaru masu yawa suna amfani dashi(DT), Kudin kasar Tunusiya yayi ta daraja har saida yayi karfi da matukar daraja a tsakanin kudaden kasashen Africa.
Wannan ya faru ne bisa tsauraran matakan amfani da kudin da kasar ta sanya wajen hana canja dinar da wasu kudade sannan aka haramta safararsa daga cikin kasar ko daga wajen kasar, wannan shine ya maida dinar yin matukar daraja a Africa.
1) Libyan Dinar (LD)
Dole mutane su girgiza tare da mamakin yadda kudin Libya year karamar kasa yafi kowane kudi daraja a gabaki dayan kasashen Africa, Libyan dinar yana daga cikin kudade masu darajar dake kalubalantar darajar Dala a Africa
A yanzu haka LD 1.41 dai dai yake da dala daya, Sannan a karkashin wani shiri da babban bankin kasar Libya ya fitar,bankin ya iyakance adadin dalar da za'a rika canjarwa ga yankasa. Yadda shirin ke aiki shine gwamnatin Kasar Libya ta gano gaskiyar karuwar Dinar shine ambaliya da dala keyi ne zuwa Libya. A wani rahoto da aka fitar an bayyana cewa dalar America million goma($10 million) ke shiga cikin Kasar ta hanyar bakaken kasuwanci da akeyi a kowace rana, hanka kuwa yana faruwa saboda babban bankin kasar na fitarwa kowane Dan kasar alawus daya kai dala Dari hudu ($400) da dala a maimakon dinar a duk shekara.
Comments
Post a Comment