Kungiyar matasan arewa ta gargadi yan arewa masu shirin tafiya kudu.
Gamayyar kungiyar matasan arewa yan asalin arewa sun gargadi mutanen arewa masu son tafiya yankin kudu dasu dakata ko kuma su zauna cikin shiri saboda abubuwan da suke faruwa a kudu.
Biyo bayan tashe tashen hankulan da suke faruwa a kudu na yawan takura da neman fadan da yan kudu ke yiwa yan arewa.
Sannan kuma kungiyar matasan arewan ta sake yin Allah wadai gamida tofin Allah tsine ga kone konen tare da farfasa kayan yan arewan da yan kudu ke musu a yankin nasu.
Haka kuma kungiyar matasan arewan tace tayi umarnin fadar hakan ne domin ganin an kawo karshen matsalar da take ta famar faruwa a kudun maso yamma.
Dan haka muna kira ga gwamnatin da sauran jami'an tsaro dasu daidaita lamarin, domin a tsawatarwa duk wasu masu shiri ko son tada husuma a kasa, domin ko a kundin tsarin kasar ya nuna kowa yanada damar shiga duk inda yai niyyar zuwa a cikin kasa dan haka bai dace dan yan arewa sun shiga yankin kudu ba su yan yankin suna nuna musu wariya da tsangwama ba, haka kuma bai dace suna yawan kai musu farmaki suna takalarsu da yin fada ba inji kungiyar matasan.
A yan kwanakin nan ne dai aka samu tashe tashen hankula tsakanin yarabawa da wasu yan arewa mazauna yankin kudun inda har yarabawan suka kokkonewa yan arewan kayayyaki tare da farfasa musu dukiyoyinsu da ji musu raunuka wanda hakan bai yiwa mutane da yawa dadi ba.
Wannan shine yasa kafafen yada labarai suka fara yin bore a rubuce kan cewa ya kamata a dauki mataki kar aje a samu matsalar da ba a zato.
To saidai har gwamnati ta fara magana akan tsarin cewar bazata lamunci tashe tashen hankula dake faruwa a kasar ba.
Sannan gwamnatin ta nemi mutane su zauna lafiya domin tabbatar da kwanciyar hankali a kasa.
Comments
Post a Comment