Kunji dalilin da yasa yan yankin kudu suka dauki karan tsana suka dorawa hausa fulani ne?
Akwai ciwo matuka da tada hankali wajen irin wannan tsananin kiyayyar da yarbawa da inyamurai ke nunawa mutanen yankin arewa ma'ana hausa fulani, wanda hakan ko kadan ba adalci bane.
Tun kafuwar kasar Nijeriya ake samun irin wadannan nuna tsanar da tsantsar kiyayyar a tsakanin yan kudu yarabawa da inyamurai ga mu yan arewa hausa fulani.
Koda yake idan mukai nazari suna nuna mana hakane saboda mun fisu yawa kuma mun fisu rike manyan mukamai ne cikin kasa shine yasa suke nuna jin haushin su a kanmu.
Suna nuna bamu isa komai ba idan muka shiga yankunan su sannan suna yi mana yadda suka ga dama ta hanyar jifanmu da munanan kalamai amma su a yankin mu sunzo suna gina manyan gidaje sannan an basu yancin da mu ba'a bamu ba kawai domin son zaman lafiya.
To amma mu sunki aminta damu mu zauna a yankunansu haka kawai sai suna takalarmu da fada sannan su kashe mu tare da kone mana kayayyaki dan kawai sunga muna samun wasu abubuwa a yankinsu wanda mu in sunzo mana namu yankin bama musu haka.
Ku duba abinnan daya faru kwanan nan a jihar Oyo baiyi mana dadi ba haka kawai su kama yan uwanmu yan arewa su kashe tare da kone musu kayayyaki sannan kuma suna kokarin tashinsu daga gurinda suke.
Idan mukai duba wannan ba abu ba iya ga media kadai ya kamata ana maganar ba har abin ya fice, yana da kyau gwamnati da manyan masu ruwa da tsaki su shiga maganar ya kamata a yiwa tufkar hanci sannan mutanen da aka yiwa wannan asarar yanada kyau a biyasu kayansu da aka kone ko aka fasa ko aka lalata.
Domin na tabbata in sune akaiwa wannan to sai gwamnati ta biyasu, mu mene zaisa baza a biya namu ba? Idan za a takura musu su biya to za suna jin tsoron sake aikata irin wannan laifin da suke yawan aikatawa.
Comments
Post a Comment