Malam Abubakar Mahmud Gumi ya gana da dogo rikakken shugaban yan bindingar nan na Jihar Neja
Malamin addinin musuluncin nan da yake shiga jeji domin yin wa'azi da yan bindingar da suka addabi kasa yauma ya zauna da wani rikakken shugaban yan bindigar nan na iyaka da birnin gwari dogo gide a jihar Neja.
A kokarinsa na ganin an sasanta da yan bindingar, hakika wannan aikin da malamin yake ba karamin kokari bane kuma haka ake son duk wani yana yi.
Cikin ikon Allah tun daga lokacin da malamin ya fara shiga jejin yana yiwa yan bindingar nasiha wasu da dama sun ajiye makamansu yayinda da yawa daga cikinsu suka dauki alkawarin baza su kuma aikata irin wadannan munanan laifukan ba.
Yanzu dai kusan satar mutane da rikicin yan bindingar kusan shine abinda yafi addabar kasar har takai ta kawo mutane basu son yawan tafiye tafiye masu nisa saboda masu satar mutane.
Comments
Post a Comment