Min menu

Pages

Malaman addini suke bada gudunmawa wajen tabarbarewar wasu abubuwa a kasar nan inji gwamna masari

Malaman addini sune ke bada gudunmawa wajen tabarbarewar wasu abubuwa a kasar nan inji gwamna masari



Malamai da limamai kune fitilar gyara al'umma ke  hannun ku, idan ku ka gagara ba da hasken, wutar ku ta fi ta mu yawa, da tsanani.



Mai girma gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa malamai da Limaman Juma'a sun taimaka matuka wajen lalacewar alammuran rashin tsaro da jihar Katsina da kasar baki daya ke fama da shi.


Mai girma Gwamnan wato Masari ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani ga malamai da limaman juma'a na jihar Katsina da Ofishin Mai baiwa gwamna shawara ya shirya a dakin taro na hukumar kula da ma'aikatan kananan hukumomi da ke hanyar Kaita cikin garin Katsina.


Ya kara da cewa malamai da limaman ku ne fitila da ke haskawa al'umma, kun fi kowa dama saboda kusancin ku ga al'umma, Aminu Masari idan ya yi magana dan siyasa ne, amma kun ba da guddumuwa wajen lalacewar al'ammurra. Wa'azi ba fuska ya ke kallo ba, domin wa'azi da aka yi shekara dubu daya da dari hudu da suka wuce, da ba'a yi shi ba kenan, don za ka ga addinin musulunci ya yi dai dai da yanzu. Amma an bar yara yayan mu suna abinda suka ga dama, suna haddasa fitina cikin al'umma, maimakon a maida hankali wajen yi masu da'awa, idan akwai sanin yadda jinin dan uwanka musulmi yake, ko hakkin wanda aka kashe, wadansu abubuwan ko ba'a bar su duka ba, an samu saukin sosai a kasar nan. Haka zalika, mu jihohin da abun ya shafa muka ki maida hankali da hada kai a wajen kawo karshen matsala, ga shi yanzu abun ya kara ta'azzara, yana so ya fi karfin mu a halin yanzu, saboda yara da yawa sun kara shiga harkar. Da yawa cikin fulanin mu wadanda ba mabarnata ba, sun yi hijira wasu na Gombe da jihar Bauchi, sun tsorata sauran dabbobi sun kora abun sun tafi, saboda can matsalar ba ta ta'azzara ba, kamar jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sokoto.


Gwamna Aminu Bello Masari ya cigaba da cewa yanzu wannan masifa ta satar mutane, da ta zama ruwan dare, wadda ta shigo birane, kuma a biranen ne ake da masu iya biyan kudin fansa, duk masu wannan sana'a a duk inda suke a duniya da masu saida makamai hankalin su ya dawo Nijeriya saboda arzikin da Allah ya hore mana. Kuma nan ne za'a saci mutum ya biya kudin fansa na miliyan goma zuwa ashirin har zuwa dari, dukkan kasashen Sahel din nan babu mai iya biyan Sepa miliyan dari, ai sai dai su kashe wanda suka sata, saboda babu arziki. Arzikin a Nijeriya yake, amma mun 'yan Nijeriya mun godewa arzikin da Allah ya yi mana? Ai ba mu gode ba. Ba abinda muka iya sai zagi, saboda an mance waccan masifar ta baya, da saukin ya zo kuma an ki gode masa. Ko mutum idan yana ba ka, ba ka godewa ai zai bar baka.


Masari ya ce anan malamai na da gagarumar rawa da za ku taka, kar ku kalli fuskar Sarki ko gwamna Aminu. A yi wa kasar ba Aminu ko Sarki ba, saboda mu kamar wani abu ne da zai zo ya wuce,kamar yadda aka yi wasu kafin mu zo. Amma kowa yana so ya bar abun kirki da ya yi ake tunawa da shi, a dunga tuna shi ana cewa Allah ya sa albarka. 


Daga karshe ya jawo hankalin malamai kan Ladabin wa'azi a kan munbari, malamai kun fi mu sani saboda ba halittar da ta kai Manzon Allah SAW, amma Allah ya ce ya kira ga mutane cikin hikima, balle kai ko ni. Ita hikima maanar ta tana da yawa idan aka buda ta. Don Allah ku maida hankali wajen jawo hankalin matasan nan na mu, su san wanda aka hada kaikai aka saci wani to hukuncin su duk daya ne da wanda ya sata din. Malamai ku fitilar ke hannun ku, idan ku ka gaza ba da hasken wutar ku ta fi ta mu yawa!


Sama da malamai da limaman juma'a guda dari biyu ne suka samu halartar taron na wayar da kai da kuma horaswa ta kwana biyu da Ofishin Mai baiwa gwamna Masari shawara kan harkokin tsaro ya shirya. 

An zabo Malaman daga mabanbanta akidu dake lungu da sakon jihar Katsina.

Allahu ya kare kasarmu.

Comments