Albishir mai dadi ga yan Nijeriya masu tafiye tafiye a motoci zuwa jihohi daban daban
Wani abu mai dadi ga yan Nijeriya da suke bin manyan hanyoyi wajen tafiye tafiye cikin kasa da kuma shiga lunguna da sakuna na cikin kasa.
Ministan yan sanda Muhammed Dingyadi yace gwamnatin tarayya zata samar da manyan camerori ta sanya su akan manyan titunan dake fadin kasar.
Yace wannan yazo ne cikin wani kuduri na kawo tsaro ga mutanen dake tafiye tafiye a kasar sannan kuma hakan zai taka rawar gani wajen dakile shirin masu garkuwa da mutane wanda suka fitini manyan titunan dake kasar.
Muhammed Dingyadi ya fadi hakan ne ranar talata a wata shira da suke da wani gidan talabijin, yace gwamnati ta karbi Wannan kudurin harma sun fara maganar da wani kamfani na NPS a game da tsarin na sanya camerar ta CCTV.
Mun riga mun fara maganar harma tayi nisa wanda aikin zai fara kankama nan da kankanin lokaci inji Muhammed Dingyadi din.
Ministan yace yin hakan ba karamin fa'ida zai kawo ba na ganin an dakile shirin masu garkuwa da mutanen da suka damu kasar.
Sannan ya kara da cewa za asa CCTV camera dinne akan manyan titunan dake fadin kasar, wanda daga ranar da aka sanya wadannan camerorin shikenan domin munada hanyoyin da za mu kama mutane masu garkuwa da suka addabi mutane.
Comments
Post a Comment