MATSALAR TSARO: Sama Da Kauyuka 20 Na Karamar Hukumar Faskari A Jihar Katsina Sun Zama Kufai
Sakamakon rashin tsaro da karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, sama da kauyuka ashirin sun tashi kwata-kwata babu kowa a ciki ya zama Kufai, mutanen garuruwan sun tsere ko dai cikin garin Faskari ko Dandume ko kuma suna gudun hijira a cikin jihar Zamfara.
A wani bincike da
RARIYA ta yi ya nuna cewa kusan shekara biyu zuwa yanzu, a kalla garuruwa talatin da shidda ne babu kowa a ciki, saboda yawan kai hare-haren 'yan bindigar da suke yawan kaiwa a yanki na su.
Wani mazaunin garin Faskari, wanda bai bukatar a ambaci sunan sa, saboda dalilin tsaro ya shaidawa RARIYA cewa garuruwan da babu kowa a karamar hukumar Faskari sun fi talatin da shidda a halin yanzu, saboda ko shekaran jiya sun kwashe sama da mata sha bakwai a wajen garin Maigora, har zuwa yanzu suna hannun yan bindigar.
Ya ci gaba da cewa duk ranar Allah sai wadannan yan bindigar sun kai hari a kauyukan karamar hukumar Faskari, sun kashe mutane ko sace masu dukiya da kuma yin garkuwa da su. Da karfin tsiya sun talauta mu, sun kashe mutane da dama.
Shima wani mai sharhin al'ammurran yau da kullum kuma dan asalin karamar hukumar Faskari ya ce abun ban takaici, kamar babu wadanda muka zaba a zauren majalisar jiha da ta kasa, sun yi shiru abun su. Babu wanda zai mike ya gabatar da kudurin halin da al'ummar kauyukan karamar hukumar Faskari suke ciki, duk da kuri'un mu ne, amma ko jaje ba ka ganin sun zo yi mana. Dole mahukuntar jihar nan su tashi domin kare lafiya da dukiyoyin al'ummar da suke wakilta, don gaskiya muna cikin mawuyacin hali.
Ga Wasu daga cikin garuruwan da babu kowa, ko kuma mafi yawan mutanen sun yi gudun hijira sakamakon yawan kai masu hare-haren da yan bindigar ke yi ba kyafkyaftawa a kauyukan karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina:
Birnin Kogo
Gidan Gwamma
Kurar Mota
Ruwa Kusa
Unguwar Bika
Gidan Wakili
Sabuwar Ungawa
Unguwar Gaga
Shuwaki
Unguwar Kwalle
Unguwar Mai Jakkai
Farin Dutse
Unguwar Alhaji Mani
Jar kuka
Gidan Diyam
Kogon Kura
Gidan Mukyadali
Unguwar Doruwa
Zamfarawa
Yamfa
Gidan Sharo
Makera
Yan Nasarawa
Unguwar Maidawa
'Yar Tsamiya
Kahi
Unguwar Gwanki
Unguwar Bakwai
Wadannan jerin sunayen kauyukan, mafi yawa daga cikin su al'ummar garin sun tashi ko kuma kusan ba kowa, sun tafi gudun hijira ko dai a cikin garin Faskari ko Dandume ko Funtua ko kuma jihar Zamfara, cewar wani mai sharhin al'ammurran yau da kullum dan asalin yankin.
Comments
Post a Comment