Min menu

Pages

Munanan abubuwa guda biyar da zasu samu mutanen Duniya (idan bishiyoyi sukai karanci)

Munanan abubuwa guda biyar da zasu samu mutanen Duniya (idan bishiyoyi sukai karanci)

Manyan labarai

Kalli abinda shugaban kasar America yace zaiyiwa musulman Duniya

Yadda budurwa zata kamo zuciyar saurayi cikin kankanin lokaci

Shin ka taba tunanin yadda duniya zata kasance idan babu bishiyoyi?. 



Ka gwada rufe idanunka kayi hasashen yadda duniya zata zama idan babu bishiyoyi. 

Bishiyoyi nada matukar tasiri cikin rayuwar halittun duniya bawai kawai don muna samun itacen girki ba daga garesu ko katakwan da muke kera gidaje,jirgin ruwa dadai sauransu. Kimiyya tayi nisa wajen binciken abubuwa wadanda kan iya samun mutane matukar babu bishiyoyi. A duniya akalla akwai bishiyoyi biliyan 400, a yayin da mutanen duniya suka kai a kalla biliyan 6.7, Wanda idan mutum yayi lissafi ya kama kowane mutum a duniya zai kasance yana da bishiya guda sittin.



Sare gandun daji ne babbar matsalar da rayuwar tsire ke fuskanta  bayama a guraren da akafi fuskantar Saran bishiyoyin ba tare da shuka wasu ba a madadinsu. Binciken kimiyya ya kawo wasu abubuwa hudu (4) munana da zasu iya faruwa matukar bishiyoyi sukayi matukar karanci.



1. Gurbatar iskar shaka: Idan akace babu bishiyoyi mutane bazasu iya rayuwa ba domin kuwa baza'a sami ingantaccen numfashi ba Wanda mutum zai rayu dashi, domin anan bishiyoyi sune suke fitar da sinadarin iskar da muke shaka mai kyau a matsayin numfashi (oxygen). Wannan iska itace take shiga cikin jikinmu ta kakkarya sinadaran abinci ta zakulo guba a matsayin carbon dioxide (CO2 )sannan ta taimaka mana mu amfana da abinda mukaci. Bishiyoyi nada matukar tasiri wajen sarrafa CARBON na cikin CO2 da muka fitar kuma yake yawo cikin iska ta hanyar daukan CO2 izuwa cikin jikinsu domin samun  sinadarin  CARBON din kadai bayan yabi wasu hanyoyi sai a sami sinadarin O2(iskar da muke shaka domin mu rayu). Sinadarin CABON shine abu na biyu wajen amfani a rayuwa bayan ruwa. Tsirrai gabadaya suna samun abincinsune daga hasken rana a yayin da suke samun sauran sinadarai kamar CARBON wajen gina gangar jikinsu wanda hakan yasa kullum suke girma da sauri sama da dabbobi ko mutane. Bayan tsirrai sun dauki sinadarin CARBON daga abin da muka fitar daga numfashi wato (carbon dioxide) sai kawai su fitar oxygen (O2) muma mu shaka mu rayu. Anan nasan wani zai iya tunanin kowace irin iska ma  ta isa a shaka tunda  ko a sahara babu bishiyoyi isassu amma kuma wasu halittu na rayuwa, suna rayuwa ne kawai daga sinadarin iska mai karanci sabanin wanda ke kusanci da muhallin bishiyoyi ,sannan yana dakyau kowa ya sani ko a sahara ba bishiyoyi ne babu ba karanci sukayi don haka halittun wajen basu fiya lafiya ba ko da sun rayu kuwa. Don haka kowa ya sani rikakkiyar bishiya mai ganyayyaki zata iya samar da iskar shaka(Oxygen) na tsawon shekara ga mutum goma haka kuma a duk lokacin da sinadarin CO2 yafi na O2 yawa a cikin iska tofa an sami matsala domin sinadaran guba  dake yawo a iska zasu addabemu dadi da kari zafi yawaita, cututtuka zasu fusata , garkuwar jiki zatayi rauni dadai sauran masifu.



2. Macewar kasar noma: idan rashin iskar shaka bai kashe  mutane ba a sanadiyar saran gandun daji, annoba ta gaba zata saukane kawai akan kasar noma. A wani bayani da kungiyar abinci da noma (FAO) ta fitar tace a kalla  mutane biliyan 2.5 ne a duniya rayuwarsu ta dogara  kacokan wajen yin noma. Hakika idan sare gandun daji ya samu waje a ko’ina to dukkannin wajen da matsalar tafi yawa mutanen  zasu wahala domin kuwa kasar da muke noma akanta zata cika da gurbatattun sinadarai wanda mafi akasari bishiyoyi ne ke tace su. Dadi da kari zaizayar kasa ma kadai saita dami kowa domin fasalin kasa ko siffarta zai canja ta yanda ramuka zasu yawaita, taki zaiyi karanci daga nan kuma harkar noma zata karye yunwa ta rika kashe mutane.

3. Munmunan fari: Karancin bishiyoyi a waje zai iya jawo mummunan fari, a lokacin rani bishiyoyi suna tsara yanda zasu tara datti ta hanyar zubar da ganyayyakin su domin su rage yawan ruwan dake fita daga jikin ganyayyakinsu. Duk wuraren da aka Sare bishiyoyi akwai yiwuwar lalacewar amfanin gonar da ake nomawa. Isassun bishiyoyi na bayar da iska mai cikakkiyar raba ko iska mai sanyi.

4. Karancin kayan da akayi daga bishiyoyi: Idan har babu bishiyoyi babu wani abu da za'a samu da aka kera daga garesu kamar Takardu,fensir,robobi, jiragen ruwa dadai sauransu.

5. Karancin ruwa: Duk lokacin bishiyoyi sukayi karanci a waje,ruwan sama sai yayi karanci koma ya tsaya baki daya kamar a sahara, haka kuma ruwan karkashin kasama sai yayi karanci domin jijiyoyin bishiyoyi suna matukar taka rawa wajen zuko ruwa ya taso sama ta yadda idan aka tona za'a sameshi a kurkusa


Comments