Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Zanna Muhammad amatsayin shugaban yan sanda na kasa
AIG Zanna Muhammad shine Buhari ya nada a matsayin sabon shugaban yan sanda na kasa, biyo bayan ritaya da shugaban yan sandar wato Adamu Muhammed Abubakar yayi a ranar litinin bayan ya shafe shekaru talatin da uku yana aiki, inda ya fara aiki a 1 ga watan biyu na shekarar 1986.
AIG Adamu Muhammed ya bayar da rikon kwarya ga DIG Sunusi Lemu kafin shugaban kasa Muhammed Buhari ya nada wani a matsayin shugaban yan sandar kasar.
Tsohon shugaban yan sandar yayi umarni ga DIG Sunusi Lemu daya kula da komai na bangaren yan sandar kafin a nada sabon shugaban. Majiyar tace tsohon shugaban yan sandar bawai ya bada komai bane ga lemu yadai ce ya dan rike mukamin ne na dan wani lokaci.
Shugaban yan sandar daya sauka an saide shi wajen aiki da gaskiya da rikon amana sannan yana aikinsa bisa doka da ka'ida hakan yasa mutane da dama kanyin kewarsa sannan kuma sukai farin ciki na ganin ya sauke nauyin daya rataya a kansa.
Sannan suka fara yiwa sabon da zai gajeshi fatan samun nasara aikin da zaiyi.
Suka ci gaba da yin maganganu da fata mai kyau ga sabon shugaban yan sandar kasar sannan suke ta addu'ar Allah ya bashi damar yin aiki da gaskiya da amana sannan kuma ya bashi damar kawo canji mai amfani ga kasar baki daya.
Masoyan Nura m Inuwa sun fara zanga zanga
Masu kudi bakwai da aka binne su da dukiyoyinsu
Comments
Post a Comment