Mafiya yawan Sojojin kasar Nijeriya basu ji dadin kalaman malam Gumi ba
Sanannen malamin addinin Musuluncin nan wanda ke zaune a garin Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya zargi sojojin Nijeriya da cewa ba sa son matsalar tsaro ta kare saboda suna amfana da ita, musamman makudan kudaden da ake ware wa bangaren tsaron. Inji shi.
Sai dai ko kadan da alamun kalaman nashi bai yi wa sojojin Nijeriya dadi ba kamar yadda mai magana da yawun sojojin kasar Birgediya Janar Mohammed Yerima ya shaidawa manema labarai.
"Muna matukar girmama Sheikh Dr. Ahmad Gumi, amma abin kunya da takaici yana fadar irin wannan maganar".
Ya kara da cewa "Ko kadan sojojin Nijeriya ba su da nufin cutar da kasar su da kuma al'ummar cikinta, burinmu mu tabbatar da cikakken tsaro a kasar". Inji shi
Kwanan nan dai Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya ziyarci dazukan hanyar Abuja da Kidandan da dazukan Zamfara da Sakkwato da Kebbi domin yin sulhu da 'yan bindiga tare da yi musu nasiha.
Lamarin da wasu suke ganin zai iya haifar da da mai ido.
Comments
Post a Comment