Min menu

Pages

Wani matashi ya tono wani abinda ya girgiza shi lokacin da yake tona rijiya a gidansu

 Bayan ya tona rijiya kafa dari da goma maimakon yaga ruwa sai yaga abinda ya girgiza shi.



Wani matashi dan Nigeria a jihar Inugu a cikin shafinsa na twitter ya wallafa hoton abinda ya samu a lokacin da yake tona rijiya a garinsu.


Abune mai matukar wahala a wasu jahohin kudancin Nijeriya samun ruwa mai kyau da za asha a lokutan rani, mutanen da basu da kudi ko kuma rufin asirinsu bai kai su iya tona birtsatse ba a gidajensu to dole suyi tafiya mai nisan zango domin su samu ruwa mai kyan da za su iya sha.


Ba abune bako ba, mutane a wannan yankin suyi tafiya mai nisa amma daga karshe su kare a diban ruwa a tafki ko rafi domin su sha kuma su dafa abinci.


Ikemba zaza yayi rubutu a shafinsa na twitter inda yake bayyana yadda yaci karo da wasu abubuwa a lokacin da yake hakan rijiya a kauyensu dake jihar Inugu, ikemba yace baiyi tono wanda ya wuce a kalla kafa dari da goma ba amma sai ya sami wannan abu.

Duk da yake Inugu ba ita bace jaha Wanda ke fuskantar matsalar ruwa ba lokacin rani, mutanen kauyuka da dama  domin samun kyakykyawan ruwa, a lokacin rani sukan tanadi ma'adanan ruwa domin karancinsa.

A wadannan bangarori masu matsalar ruwa yana da matukar wahala a sami mutum wanda ke iya wanka sau biyu ko sama da haka da rani.

Sana'ar saida ruwa itace sana'a mai kyau idan har zaka iya adana ruwa mai kyau a wannan yankin, kusan jarka gallon daya na ruwa ana saidashi naira hamsin a lokacin rani.


Inugu jiha ce da akai mata take da jiha mai sinadarin coals saboda ana samun coals mai yawa a wajen.

Matashin mutumin wanda ya wallafa hotunan ya bayyana yadda suka tono abubuwan a karkashin kasa, maimakon su samu ruwa sai suka samu sinadarin coals. Yace abin baiyi mini muni ba saboda zan sami kudi daga wannnan coal bayan na sayar dashi.


Coals ana amfani dashi ne wajen gina tituna, Al'amari a Najeriya a yanzu yakai matukar daya kamata gwamnati ta samar da abubuwa more rayuwa a yankuna irin wadannan domin kare lafiyar su da rayuwarsu.

Comments