Wuraren biyar masu matukar hadari a Duniya na daya dana hudu sune suka fi tsanani
Akwai wurare da dama da mutum zaiso ace ya ziyarcesu saboda matukar kyansu tare da dadin ganin da za'a iya cewa aljannar duniya ce a wajen.
A yayin da ake maganar kyawawan wurare sai maganar wurare masu masu kyau amma masu matukar hadari ta bijiro wanda idan da za'a ce mutum ya ziyarci wasunsu kyauta zaice a'a a barshi ya yafe saboda matukar hadarinsu ba tare da duba da kyawunsu ba.
Anan zamu kawo muku wurare 10 Mafiya hadari a Duniya da wasu zasu so su sansu domin da an ambacesu za'a shiga mamakin jin sunan su.
1) Titin Mutuwa- Titi mafi girman hadari a duniya:
Titin arewacin Yungas wanda akafi kira da "Titin Mutuwa" Tuki zuwa sama ko kasan wannan Titi yakai mile 43 Wanda yayi daidai da kilomita 69, komawa da baya akan wannan Titi shine mafi girman hadari domin tsananin guguwa da hazo,santsi, kwararowar ruwa tare da mirginowar duwatsu daga hawan daya kai kafa 2,000 (mita 610 ) a Duk juyowa.
Har zuwa 1994, direbobi sama dari uku sai sun mutu a duk shekara, wannan shine ya tabbatar da lakabin sunan Titin da Titin Mutuwa sannan yasa Titin Zama daya daga cikin wurare mafiya hadari a duniya.
Titin yanada matukar tsawo wanda ya hada da jejin dake dauke da dogayen bishiyoyi, har zuwa ga cikin birni.
Yana kuma zagaye da manya manyan tsaunika, wanda hakan yake nufi yan kasuwa ba safai su iya haddace ko sanin yadda motocinsu na daukar kaya zasu iya wucewa ba a kokarinsu na sayar da katakon su, da kuma abinci a wajen.
Titin ya daga sama sannan bashi da wani fadi sosai haka kuma yayi mummunar baudewa, saboda karancin fadinsa kuma manyan motocin kaya ke fadawa direbobin su mutu kayan dake cikin motocin su salwanta.
2) Lardin macizai- wajen dayafi kowane waje kisa a duniya:
Akwai Wani lardi mai tazarar da takai mile 25 daga Kasar Brazil kafin teku, wannan waje ba'a taba samun Wani yayi tafiya ba a cikinsa. An taba yada jita-jitar cewa mutum na karshe daya kusanci wajen Wani masunci ne,wanda ance bayan kwanaki an sami jirginsa na tangal-tangal a bakin gaba a mace cikin jini. Lardin wanda siffarsa keda wahalar bayyanuwa ana kiransa da sunan Ilha da Queimada Grande.
Bayanai sun tabbatar da cewa saka kafa a wannan waje nada matukar hadari, hakan yasa gwamnatin Kasar Brazil ta haramtawa mutane kaiwa ziyara wajen.Lardin na fuskantar tsananin barazana daga jinsin macizai kala-kala masu hadari masu mahaukacin dafi da hakora masu karfi.
3) Hamadar Danakil- Wajen da dutsen wuta yake:
Wannan waje na daga cikin wuraren ba'a sabawa da yanayin su a duniya, Danakil- yana gabashin, ma'aunin yanayi a wajen a kowane yana kaiwa sama 50oc, bakaken duwatsun dake wajen na fitar da bakar iska mai guba. Hamadar Danakil ba waje ne da mutum zaiyi sha'awar zaiji zuwa ba domin zahirin lafiyar mutum a cikin kankanin lokaci zata gurgunta.
Mummunan tasirin da yanayin ke fitarwa a sanadiyar Aman guba da duwatsun wajen ke fitarwa yana fitar da sinadarin sulfur. Bangaren dake aman gubar na daga cikin bangaren daya maida shi daya daga cikin wurare masu matukar hadari a duniya.
4) Lardin arewacin Sentinel - Haramtacce, mai hadari sannan waje mai wahalar bayyanuwa:
Dalili na biyu daya saka aka hana kai ziyara wajen saboda lafiyar Lardin.
5) Wajen shakatawa na Madidi- Dausayin Aljannar duniya:
Wajen shakatawar Madidi yana tsakanin Kogin Amazon dake Bolivia sannan yana da girman akalla murabba'in kilomita 19,000. Dausayin Madidi surkukin dajine wanda ke cike da kala-kalan tsirrai da kuma dabbobi wanda wasu daga cikinsu suna da matukar hadarin gaske. Dajin a cike yake da muggan halittu wanda saboda su ake baiwa kowane mai ziyara a wajen duk abin daya sameshi a ciki nauyin yana kansa.
Dajin yana daya daga manyan gandun daji a duniya da ake kula dasu soboda halittu masu hadari dake cikinsu.
Comments
Post a Comment