yar shekara goma sha biyu sukaiwa fade su bakwai sannan suka ce ba a isa ai musu komai ba.
Bbc Hausa ya wallafa a shirinsu cewar wasu magidanta har kimanin su bakwai ne sukai wa wata karamar yarinya wacce duka duka shekarunta baza su wuce bakwai ba fyade a jihar Sokoto ta Nigeria.
Inda mahaifiyar yarinyar da aka aikatawa wannna mugun aikin take cewa cikin mutanen da sukai wannan aika aikar ga diyar tata har cewa yayi zai kasheta idan bata amince ba a lokacin.
Bayan ya gama lalatar da ita da karfi ya mikata ga sauran yan uwan nasa suma suka gabatar da mugun nufin nasu a kanta.
Mahaifiyar yarinyar tayi kokari ganin anje kotu ita da sauran mutane saidai koda aka je kotun mutanen da suka aikata lefin sai aka ce za a turasu gidan yari tukun domin baza a yanke musu hukuncin laifinsu yanzu ba.
To amma kafin a kaisu ga zuwa gidan mazan an sake su sunata yawo a cikin unguwa har kirari suke suna cewa ai shari'a ta kare babu wani abu da za ai musu.
Harda wanda yake zuwa yana tsayawa a kofar gida yana dariya yana cewa ai shari'a ta kare babu abinda zai faru inji mahaifiyar yarinyar.
Yarinyar marainiya ce duka shekarunta basu haura goma sha biyu ba kuma ganin wannan mummunan aikin da aka aikata mata yasa take samun tsangwama ga sauran mutane harma karatun ta ya tsaya saboda koda ta fita har nunata ake.
Mutane da yawa sun tausaya tare da nuna rashin jin dadinsu na wannan rashin adalcin da akaiwa yarinyar karama kuma marainiya.
Yayinda a bangaren mahaifiyar ta take cewa tana cike da tsoro da fargabar wani abu ka iya faruwa ga diyar tata domin akwai samari masu irin wannan halin, kuma sunga anyi abu ga yarinyar ba tare da an dauki wani mataki ba suma zasu iya yi mata komai.
Irin wadannan munanan ayyukan suna yawan faruwa tsakanin al'umma kuma sai kuga anyi abin ba tare da an dauki wani mataki ba wanda hakan ba karamin matsala yake haifarwa ba.
Ya kamata duk lokacinda aka samu irin wannan case din gwamnati ko kuma manyan mutane masu kudi su shiga ciki domin ganin an hukunta mai laifin da ya aikata wannan laifin.
Wanda hakan shine zaisa sauran dake da burin aikata irin hakan su kasa aikatawa.
Wanda yin shirun da kuma yin biris da ake in haka ta faru ka iya sawa mutane suci gaba da aikata laifukan domin sun san babu abinda zai faru koda sunyi hakan.
Kuma ya kamata mutanen gari su hankalta suna taka tsantsan da saka ido akan mutanen da basu yarda dasu ba a unguwa sannan suna yawan bincike ga duk wanda basu aminta dashi ba.
Comments
Post a Comment