Tun Lokacin da Gwamnatin kano ta sanya ranar yin muqabala ta qeqe da qeqe da Abduljabbar kabara Daliban shi Abduljabbar kabara suke ta yin azumi da kwana sallar dare da karatun kur'ani da dafa abinci suna ciyarwa da tara mutane suna basu sadaka
Duk suna yin haka ne don Allah ya ba wa Malaminsu nasara a wannan muqabalar ta qeqe da qeqe da za'ayi
Don haka na ke kira ga "Yan uwa ahlussunnah akan mu ji tsoron Allah mu kiyayi kuri da fariya da cika baki da Rantsuwar cewa mu ne zamu yi nasara game da wannan muqabalar Kar mu yi abin da Allah baya so mu dage da yin addu'ah da neman temakon ubangiji
Shin bama tunanin Allah zai iya jarrabarmu? Mu tuna yaqin Badar Annabi S.A.W. ba fariya da cika baki ya yi ba temakon Allah ya nema haka a yaqin hunaini Allah S.W.A. ya jarrabi sahabbai R.T.A. har aka samu wasu suka gudu abin da ya janyo musu haka ganin suna da yawa sai suke ganin kamar su za su yi nasara a yaqin ita Nasara a wajen Allah ta ke mudai mu yi riqo da sababi domin shi Allah ba'a yi masa dole kuma baya son masu fariya
Mu dai muna kyautatawa Allah zato Gaskiya ce za ta yi Rinjaye akan karya don haka mu yi addu'ah mu yi ikhlasi mu kyautata niyyah inshaa Allah zamu yi nasara sannan kuma Gwamnati ta ce muqabala za'ayi ta babu fashi duk da janyewa na qin zuwa da Sarkin musulmai da kungiyar JNI suka yi
Muna Addu'ar Allah ya temaki gaskiya da masu kira akan gaskiya ya ba wa Gaskiya rinjaye akan karya ya rusa makaryata maha'inta ya kunyata su ya yi mana maganinsu.
Comments
Post a Comment