Min menu

Pages

Abin ya dawo magidanta kuyi hankali da matanku

An kuma!Wani mutum yayi nasarar kufcewa mutuwa a hannun matarsa saidai duk da haka tabar masa abinda bazai manta da ita ba



A ranar 8 ga watan Maris din wannan shekarar ne aka sami labarin wata matar aure mai suna Bisola Awolede bisa zargin watsawa mijinta tafasheshshen ruwan zafi a jiki. 


Yan sandan jihar Ogun sun bayar da bayanin kama matar ta bakin mai magana da yawun yan sandan yankin da al'amarin ya faru DSP Abimbola oyeyemi, Oyeyemi yace  sun kama matar da ake zargin bayan da mijinta Peter phillips ya ruga zuwa ofishin yan sanda dake  sango yankin ota yakai rahotan abin daya faru tare da Mummunan kunar wuta a jikinsa, Peter yace matar tasa Wanda take da 'ya'ya biyar tayi zarginsa da shan giya sannan ta dauko ruwa mai zafi Wanda yake tsakar tafasa ta zuba masa a jiki.

Gabanin lokacin da ake bayar da rahotan shugaban babban ofishin yan sandan ACP Muhideen Obe ya bayar da umarnin fara bincikar al'amarin matar Wanda tayi kokarin kashe mijin nata da ruwan zafi, cikin kankanin lokaci suka fahimci yadda al'amarin ya faru.

A bayanan da matar da ake zargin ta bayar ta bayyana yadda mijin nata ke shigo mata gida bayan yasha barasa yayi mankas, haka kuma ko kadan bai damu da wani jin dadi da walwalarta ba ita da 'ya'yanta.

A bayaninta ta kara da cewa a ranar da wannan abin tsautsayi ya faru mijin nata ya dawo gida cikin maye kamar yadda ya saba kawai sai ya hau zaginta da iyayenta tace hakanne ya fusatata ta dauko ruwan zafi Wanda ke tafasa a lokacin ta watsa masa. 

Mai magana da yawun yan sandan Abimbola ya kara da cewa a binciken da suke an sake samun matar bisa zargin kashe jaririnta dan wata takwas cikin fushi tare da binne gawarsa cikin sirri. 

Abimbola ya kara da cewa da aka tsaurara bincike matar da kanta takai yan sanda har wajen data binne jaririn Wanda aka samu harya kumbura ya fara rubewa.


Oyeyemi ya kara da cewa a yanzu haka an tura maras lafiyar zuwa babban asibiti domin kula da lafiyarsa.

Kwamishinan yan sandan jahar Ogun ya bayar da umarnin mika wannan al'amari zuwa ga sashen manyan laifika domin bincike domin daukar tsatstsauran mataki.

Comments