Sarkin Musulmi Alh Sa'adu Abubakar ya tsame hannun sa kan batun jagorancin zaman mukabala da za ayi tsakanin Malaman jihar Kano da Abduljabbar Nasiru Kabara.
Biyo bayan sanarwar da gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin komishina mai lura da sha'anin addini a jihar kano Dr Baba Tahar ya fitar na ayyana ranar da gwamnatin jihar Kano ta yi tare da sanya Sarkin Musulmi Alh Sa'adu Abubakar a Matsayin wanda zai jagoranci zaman kwamitin mumabala a ranar Lahadi 7-3-2021 mai zuwa ne, sai ga sanarwa a yammacin jiya ta hannun Sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam cewar mai Alfarma Sarkin Musulmi tare da dukkan 'ya'yan kungiyar ba za su shiga hidimar tattaunawar da gwamnatin jihar Kano ta shirya ba.
Sanarwar ta yi kira ga Gwamnan jihar Kano da ta sauya tunanin ta kan batun zaman da ta shirya domin a cewar ta ko kadan Abduljabbar bai kamata a yi masa irin wannan kambawa ba, bayan zargin sa da suke yi kan kalaman tunziri.
Kamar yadda aka riga aka sani ne bayan korafin da majalisar Malamai ta jihar Kano ta shigar wa gwamnatin jihar Kano kan shi Abduljabbar har ta kai ga gwamnatin jihar ta dakatar da shi kan gabatar da karatuttukan sa tare da rufe masallacinsa.
DUNIYA INA ZAKI DAMU INNALILLAHI WA,INNA ILAIHI RAJI,UN SUN KASHE WANI BAWAN ALLAH AKAI NAIRA 3500
Sai shi Abduljabbar ya mika koken sa ga Gwamnan jihar kan a ba shi damar kare kan sa ta hanyar kira ga Gwamnan jihar ya hada su da Malaman da suka kawo wannan korafi a kan sa don tabbatar da Hakikanin abin da suke cewa yayi.
Hakan ne ya sa Gwamnatin jihar taga kyan hakan tare da kafa komitin gabatar da shi wannan zama don tantance Gaskiyar lamarin tsakanin Malaman jihar kano da suke ikirarin cewar Mal Abduljabbar yayi batanci ga Annabi da sahabbai.
DUNIYA A BAR TSORO CE TA KASHE ABOKINTA KADA YA TONA MUSU ASIRI
Da shi Abduljabbar dake cewar karya suke yi masa shi na hakaitar da batancin da aka yi wa Annabin ne a cikin littafa tare da kore su gare shi, da kuma tabbatar da tsarkinsa.
Comments
Post a Comment