MACIYA AMANAR TSARON NIGERIA YA FARA TONUWA
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara tayi watsi da umurnin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na sanya dokar hana shawagin jiragen sama a Jihar da kuma haramta hakar ma’adinai.
Majalisar dokokin jihar Zamfara tayi zama a yau, ta kada kuri'a akan yin watsi da matakin Gwamnatin tarayya, 'dan Majalisa Faruk Dosara shine ya gabatar da kudurin na ayi watsi da umarnin Gwamnatin Buhari
Faruk Dosara yace babu dalilin kafa dokar hana shawagin jiragen sama a jihar Zamfara, domin ba a jihar Zamfara aka fara sace daliban Makarantu ba, inda yake cewa anyi a Chibok da Dapchi da Kankara da kuma Kagara, amma gwamnatin Buhari bata dauki irin wannan matakin ba
Amma gaskiya wannan mataki da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dauka ya bani mamaki, kuma ya bani tsoro, imba sharrin tsarin Mulkin Demokaradiyyah ba wai har shugaban kasa zai bada umarni akan hanyar da za'a inganta tsaro wani bagidajen kauye yace bai yadda ba
SUN KASHE SHI TAKAN NAIRA 3500
Ba mamaki asirin maciya amanar tsaro ne ya fara bayyana, ina bada shawara wa Gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar karbe ragamar shugabanci a jihohin da suke fama da tsananin ta'addanci a ayyana dokar ta baci kawai, inda hali sojoji su mulki jihar
Lallai babu karya da akeyi cewa matsalar tsaron nan akwai sa hannun wasu kebantattun mutane, turawan da suke tonon ma'adinai suna yin kashe mu raba da su, suna taimakon 'yan ta'adda, ba zasu taba goyon bayan duk wani mataki na inganta tsaro ba
Muna kira ga hukumomin tsaron Nigeria a tsananta binciken sirri mai zurfi akan Faruk Dosara, duka lambar wayoyinsa a sanyasu cikin data base da za'abi diddiginsa
Muna rokon Allah Ya tona asirin duk wani maciyin amanar tsaro a Nigeria kowaye Amin
Comments
Post a Comment