Daurin Rai-Da-Rai Ga Wanda Ya Shigo Da Shinkafar Kasar Waje
Majalisar dokoki ta tarayya ta fara karatu na farko a wata doka da Saidu Musa Abdullahi ya gabatar wa majalisar; dokar dai tana so ne a dauki tsattsauran mataki ga duk wanda aka samu da laifin ya karya dokar shigowa da shinkafar waje cikin kasar nan.
A cikin dokar har da rayuwar dindindin a gidan yari, da kuma kwace duk abinda aka yi amfani da shi wajen shigowa da shinkafar da sauran abubuwa masu tsauri.
Gwamnatin tarayya dai ta hana shigowa da shinkafar kasar waje ne tun a zangon Buhari na farko, wanda a cewar su an hana ne domin inganta noman shinkafa a Nijeriya da kuma ba shi muhimmanci.
Comments
Post a Comment