Idan har kana amfani da Bank to zama bai kamaka ba in baka san wannan ba
Babban Bankin Najeriya (CBN) Ya fitar da sabon tsarin na cajar zunzurutun kudi har Naira 6.98 a duk yin amfani da akayi da layi wajen mu'amala ta kudi a bankuna.
Babban bankin ya fitar da wannan sanarwa a ranar talatar nan 16/03/2021 cewa za'a ciri Naira 6.98 a duk cire kudi ko turawa daga banki.
Wannan tarar kudade ta biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin babban bankin da bagarorin dake kula kamfanonin kafafan sadarwa a ranar litinin domin biyan bashin kudi Naira biliyan arba'in da biyu (N42bn) da babban bankin ke bin kamfanonin sadarwar.
Sanarwar Wanda ke dauke da saka hannun hadin gwiwa Wanda ya hada da saka hannun Darektan rukon kwarya na sadarwa na babban bankin Osita Nwanisobi da Darektan Hulda da jama'a na hukumar sadarwa na kasa Ikechukwu Adinde sanarwar tace " Bayan dogon zaman da mukayi mun sami matsaya.
Dokar zata fara aiki 16/03/2021 zatayi aiki akan kowane saka kudi ko cire kudi da akayi a banki ta hanyar yin amfani da waya.
Comments
Post a Comment