Naji dadin saka ranar muqabular nan amma fa malaman da kuka hadani dasu bazasu iya komai ba ina baku umarni ku sake wasu baza su iya ja dani ba
Mukabular da aka shirya naji dadinta domin zan nuna musu gaskiya ta inji Abduljabar
Fitaccen malamin nan Abduljabar kabara ya nuna jin dadinsa ga yan wasika da aka aika masa daga gwamnatin jiha na sanar dashi ranar da aka ware na yin mukabalar dashi da sauran malamai.
Cikin wata magana mai kama da fariya da jin kai shima ya aika takardar amincewa da zaman da za ayi tsakanin sa da sauran malaman da aka ce za suyi a kano.
Yace shi dama haka yake so suyi muqabular domin ya nuna musu tsakaninsa dasu waye mai gaskiya, yace shi yana nan akan bakansa na dukkannin maganganun da yake domin shi yasan yana kan gaskiya a cewarsa.
Naji dadin wannan tayin da akaimin na yin mukabalar dan haka naji dadi kwarai da gaske yanzu lokaci kawai nake jira.
In baku manta ba a yan kwanakin can gwamnatin kano ta rufe masallaci tare da makarantar da wannan mutumin yake domin yayi wasu furuci marasa dadi ga sahabbai wanda hakan bai yiwa duk wani musulmi dadi ba ciki kuwa harda gwamnatin kano da sauran mutane.
Hakan yasa aka yanke wannan hukuncin a kansa, to saidai ya fito yana cewa wai ba'a kyauta masa ba domin yanada hujjarsa na yin wadannan maganganun, wannan yasa gwamnatin Kano taga ya dace ta hadashi da malamai domin suyi muqabula wanda zasu nuna masa abinda yake ba haka bane kamar yadda yake cewa.
An zabo malamai daga bangarori kamar izalah da darika dadai sauransu.
Mutane da yawa sunji dadin wannan abinda da gwamnatin kano tayi dan haka yanzu ranar kawai kowa yake jira domin a bambance tsakanin duhu da kuma haske.
Allah ya nuna mana ranar lafiya.
Comments
Post a Comment