Jihohi masu fama da talauci guda goma a Nijeriya
Nijeriya kasa ce da Allah ya hore mata albarkatu da kuma sauran abubuwa na rayuwa kusan kowacce jihar tana samun dan wani abu da ta dogara dashi.
Saidai duk da haka dole wasu jahohin sunfi wasu walau ta bangaren arziki, tarin mutane, yawan masu ilimi, tarin masu kyau, da kuma yawan matalauta.
Yau muna tafe da jerin sunan wasu jahohi har guda goma da bincike ya nuna sunfi kowacce jiha a Nijeriya yawan talauci da kuma matalauta.
• Sokoto bincike ya nuna jihar sokoto tafi kowacce jihar a Nijeriya tarin matalauta, suna da wajen kashi 81.2% na matalauta.
• Katsina jihar katsina ta biyo cikin jahohin matalauta a Nijeriya domin basu da wani abu da suke fitarwa ko harkar kasuwanci da take kawo kudi wa jihar hakan yasa aka sata cikin jihohin masu fama da matukar talauci.
• Adamawa sunan jihar Adamawa ya shigo cikin jerin jihohi matalauta saboda barnar da yan boko haram sukaiwa jihar hakan yasa basa iya fitar da wasu kayayyaki ko su shigo dasu.
• Gombe sunada kashi 73.2% na matalauta
• Jigawa sunan jihar jigawa ya fito cikin sahun jihohi masu fama da talauci saidai yanzu abubuwan ya fara raguwa ba kamar da ba.
• plateau koda yake tana daga cikin jihohi masu yawan mutane da kuma sunada kabilu masu yawa amma duk da haka an aiyana jihar cikin jahohi masu fama da talauci.
• Bauchi jihar itama tabi sauran takwararta wajen talauci sai kuma jihohin benue da kebbi da Zamfara.
Wannan sune jihohi guda goma dake fama da talauci a cewar masu bincike.
Comments
Post a Comment