Min menu

Pages

Jaririyar da aka jefar tana kwana goma da haihuwa ta samu mahaifiyar ta bayan ta girma takai shekara 40, saidai akwai wani abu data fada da ya bewa kowa mamaki

 


Jaririyar da aka jefar tana kwana goma da haihuwa ta samu mahaifiyar ta bayan ta girma takai shekara 40, saidai akwai wani abu data fada da ya bewa kowa mamaki


Wata sarauniyar kyau mai suna Elizabeth wanda aka bari a tashar jirgin sama bayan haihuwa ta da kwana goma ta hadu da mahaifiyar ta bayan shekaru 40.

Elizabeth Hunterson wasu matukan Jirgi ne guda biyu suka tsinceta a bakin kofar shiga tashar jirgin Nevada a shekarar 1980, an sameta ba tare da wata alama ba wanda zata iya nunin wajen data fito. 


Duk da Elizabeth ta sami masu ruko na kwarai cikin kulawa da soyayya, Elizabeth mai shekara 41 tace ta dade tana mamakin wane irin laifi ta aikata wanda ya jawo iyayenta tana kwana goma da haihuwa suka ajiye ta kuma suka tafi suka barta.

"Na dauki tsawon lokaci a rayuwata a Duk lokacin da nayi arba da Wani mai kamata saina tambayeshi inji ko muna da alaka" cewar elizabeth.

Daga karshe elizabeth ta hadu da mahaifiyarta bayan anyi gwajin zubin halittar dan Adam wato DNA.


Elizabeth wanda aka baiwa sarauniyar kyau ta Naveda a 2004, ta gano mahaifinta na gaskiya a 2004, amma saidai ya mutu kafin yasan yarsa ce ita.

Bayan Elizabeth tayi rubutu ne zuwa ga mahaifiyar ta ta fahimci mahaifinta Bakar fatane, mahaifiyarta kuma yar asalin kasar japan ce anan ne Elizabeth ta fahimci abinda ya saka aka barta a bakin tashar jirgin sama.


Comments