Wadannan kasashen sunfi ko ina zafi a africa
A duniya akwai wasu kasashe masu matukar zafi Wanda a duk lokacin da yanayin zafi yazo mazauna cikin su ke shiga wani yanayi koma su fita a hayyacinsu.
Anan zamu kawo muku wasu kasashe masu matukar zafi a cikin kasashen Africa dan haka muje ga sunan kasashen
1) Mozambique (Tsibirin Juan de Nova)
Wannan tsibiri ne Wanda yake a mazaunin mallakin faransa tun a shekarar 1897. Juan de Nova yana kan hayar Mozambique, yana da yanayi na zafi Wanda yakai digiri 84 na Faranhait. Wannan waje na tsakanin gabashin Africa da Madagascar.
2) Kasar Chadi
Kasar chadi nada yanayi na zafi kan lamba 96 na digirin Fahranhait. Chadi na iyaka da kasar Libya ta arewa, Sudan ta gaba shi, Africa ta tsakiya daga kudanci, kamaru da Najeriya ta kudu maso yamma sai kasar Niger daga yammaci.
3) Mauritania
Kasar Mauritania tana gabar da tekun Atlantika ta Africa, ta nan wajen ne sahara ta hade da bakin gabar teku. Kasar nada arzikin ma'adanan cikin kasa mafi akasari Iron da kuma ore. Mauritania nada yanayi zafi mai lambar digiri 92.1 na Fahrenheit.
4) Gambiya
Kasar Gambiya tana da digiri Fahrenheit 82.4 na yanayin zafi. Gambiya karamar kasa ce a yammacin tekun Africa Wanda tayi iyaka da kasar Senegal ta kowane bangare. Mutane dayawa masu yawon bude ido da binciken kayan tarihi na samun mafaka a wajen garbar tekun Atlanta.
5) Niger: kasace wanda keda yanayin zafi domin duk lokacinda zafin kasar ya motsa yana takurawa mazauna yankin, sannan mutanen da tsananin zafin yafi damu sune mutanen da suke zaune gurin da yake da tsananin hamada tare da yawan rairayi. Yanayin zafin yakai digiri Fahrenheit 94.4
6)Mali: kasace wanda keda yanayin zafi na ban mamaki wanda mutane kan fita hayyacinsu wasu ma har tunanin yin kaura suke subar gurin saboda yadda zafin gurin ke takura musu. Yanayin zafin yakai digirin Fahrenheit 83.1
7) Djibouti:kasace wanda keda yanayin zafi domin mutanen dake yankin ba karamin kaduwa suke yi ba idan lokacin tsananin zafin yazo. Domin yanada digiri Fahrenheit 83.3
Comments
Post a Comment