Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi
Kugiyar The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC, ta yi kira ga hukumomin tsaro su kama Sheikh Ahmad Gumi sun bincike shi - Kungiyar ta furta hakan ne bayan Dr Ahmad Gumi ya kwatanta yan bindiga da marigayi tsohon jagorar Ibo Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu - Kungiyar ta OYC ta ce duba da yadda Dr Ahmad Gumi ke kokarin kare yan bindigan yana cewa su ba yan ta'adda bane, ya kamata a bincike shi Kungiyar matasan Ibo ta 'The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC,' ta bukaci a kama malamin addinin musulunci da ke kokarin yin sulhu da yan bindiga a arewacin Najeriya,
Dr Ahmad Gumi ya fusata kungiyar ta Igbo ne sakamakon kwatanta shugaban Ibo, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da yan bindiga a hirar da aka yi da shi a BBC Pidgin
Sun Kashe shi takan Naira 3500
Ohaneaze: Kungiyar Ibo ta bukaci da damke Sheikh Ahmad Gumi. Hoto: @TheNationNews Source: Twitter Ojukwu ne ya jagorancin kabilar Ibo yayin yakin basasar Nigeria da aka shafe shekaru uku ana gwabzawa wadda ta yi sanadin salwantar miliyoyin rayyuka, kuma na ganin laifin da Ojukwu ya yi ta yi kama da na yan bindiga. A martaninsa, Mazi Okwu Nnabuike, Shugaban OYC na kasa, ya ce ya yi mamakin yadda har yanzu hukuma ba ta kama Dr Ahmad Gumi ba. Ya ce duk da cewa akwai alamun Dr Ahmad Gumi na da 'alakar soyayya' da yan ta'addan, jami'an tsaro sun kawar da kansu sun bar shi yana yawo yayinda tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar. OYC cikin sanarwar da ta raba wa manema labarai ta ce, "Nigeria na kan gaba a tarihinta na cigaba da zama kasa daya. Ba a taba samun lokacin da ake tafka laifuka a kasar nan ba da sunan kungiyoyi bayan daban-daban.
Abinda ya fi tada hankali shine yadda mai magana da yawun yan ta'addan, Sheikh Gumi ke yawonsa duk da cewa ana iya gani karara yana cikin matsalolin tsaron Nigeria. "Ya fara da ikirarin cewa yan bindiga ba yan ta'adda bane, sannan ya kwatanta yan bindiga da IPOB yanzu kuma yana kwantanta su da Dim Odumegwu Ojukwu, babu shakka Gumi ya zama kakakin yan ta'adda don haka a kama shi a bincike shi." Sanarwar ta kara da cewa dama ba yau ya fara furta maganganu da kan iya raba kan kasa ba da tada zaune tsaye don haka ta yi kira ga jami'an tsaro su kama shi su bincike shi don haka ne kadai hanyar kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane.
Ta Kashe Saurayinta Kada ya Tona Asirinsu
Comments
Post a Comment