Mai Digiri Biyu Ya Rungumi Sana'ar Jari Bola A Jihar Katsina
Wani matashi da ya kammala digiri na daya da na biyu, Malam Surajo Yazid ya rungumi sana'ar jari bola ko kuma gwangwani domin ganin ya dogara da kansa.
Wannan matashi ya wallafa takardun shaidar kammala digiri na daya da ya yi a jami'ar Malam Umaru Musa Yar'adua dake katsina, inda ya karanta ilimin Tarihi, wanda ya kammala a shekarar 2015 da kuma digirinsa na biyu da ya yi a jami'ar Bayero dake Kano, inda ya karanci ilimin(Developmental Studies) wanda ya kammala a shekarar 2019.
Surajo Yazid ya yi takaitaccen rubutu, a shafinsa na Facebook, in da ya ce ya fi alfanu ka zauna da kafafunka da ka zauna ka lankwashe kafafunka. Na kwammace in zauna cikin datti da in zauna fes-fes ina jin yunwa. Na gode kasata wadda ke wofintar da masu kokarinta ko ilimi.
Comments
Post a Comment