Girkin mu na yau, Tuwon shinkafa Miyar wake, meat pie da kuma Garnishing macroni.
Tuwon shinkafa miyar wake
Ingredients
Shinkafar tuwo
Wake
Manja
Nama
Kifi bushashe
Attarugu da tattasai
Albasa mai ganye
Maggi
Spices
Onga
Dafarko zaki wanke shinkafar ki sai ki dora a wuta ki rufe daga nan sai ki dakko waken ki ki barza shi wato ki cire bawon dake jikin sa sai ki wanke shi daga nan sai ki dora tukunya akan wuta ki dora manja idan yayi zafi sai ki kawo albasa ki zuba da kayan miya ki soyasu.
idan suka soyu sai ki kawo naman ki da kika tafasa da ruwan naman dukka ki zuba akan kayan miyan sai ki kawo kifin ki daman kin wanke shi da ruwan zafi shima ki juye a ciki sai ki zuba waken ki rufe daga nan sai ki koma kan tuwon ki idan ya dahu ki tuka ki kwashe kisa a leda.
Toh miyar ki na ta dahuwa idan kika ga waken yayi laushi sai ki kawo komai na kayan maggi ki zuba ki kawo albasa mai lawashi kizuba sai ki rufe idan ya karayi kadan sai ki sa ludayi kidan farfasa wanke yanda kikeso kaurin sa ya kasan ce idan yayi sai ki sauke.
Meatpie
Ingredients
Mai
Baking powder
Nama
Salt
Maggi
Attarugu
Onion
Flour
Curry
Onga
Cabbage
Carrot
Spices
Ruwa
Dafarko zaki samu bowl sai ki zuba flour a ciki kisa baking powder sai kiyi mixing nasa sai ki kawo spices kizuba da curry maggi onga gishiri sai ki zuba mai kiyi mixing nasu sai ki kawo ruwa kadan ki zuba kiyi ta juyawa har sai ya hade jikin sa.
Tom sai ki samu wani abu ki rufe shi sai ki dawo kan cabbage zaki yanka cabbage naki sirisiri kanana sai ki goga carrot din ki shima dama kin tafasa naman ki already kin daka shi sai ki dora pan a wuta sai ki zuba mai kisa naman ki da attarugu da albasa da kayan maggi da spices kiyi ta juyawa
sai ki kawo cabbage da carrot din ki zuba akai kiyi ta juyawa har sai kinga cabbage din ya dan yi laushi ba sosai ba sai ki sauke ki fara murza meatpie din ki kina fitar da shape din shi idan kika gama sai ki soya.
Note idan a oven zaki gasa toh da butter zakiyi kwabin idan kuma a mai zaki soya toh da mai zakiyi kwabin ki dan sai yafi dadi.
Garnishi macaroni
Ingredients
Macaroni
Mai
Maggi
Salt
Spices
Curry
Potato
Egge
Green bean
Green pepper
Onion powder
Carrot
Onion rings
Attarugu
Kifin gwangwani
Garlic powder
Ginger
Dafarko zaki tafasa macaroni ki sai ki taceta ki ajiye ta a gefe sai ki tafasa carrot green bean da potato zaki yan ka shi kanana suma ki tace su agefe sai ki dora mai akan wuta kisa albasar ki da ginger da onion ki kawo galic powder ki zuba kina ta juyawa har sai albasarki tayi laushi kadan sai ki zuba attarugu da su carrot green bean da potato din ki soya su tare sai ki zuba maggi da spices
kijuya sai ki kawo macaroni ki zuba ki juya sai ki zuba kifin gwangwani ni a ciki sai ki kawo albasa ki kuma zubawa akai sai ki kawo egg din ki dama kin dafashi sai ki bare ki yanka akai sai kike juya wa a hankali saboda kar kifin ya bashe sai ki rufeshi na 5 minute shikenan.
Comments
Post a Comment