Mutane biyu sun mutu lokacin da fulani da yan kabilar Yoruba suke mummunan fada
Jaridar Punch ta rawaito mutuwar mutane biyu lokacin da ake wani kazamin fada tsakanin wasu fulani da yan kabilar Yoruba a kasuwar Oyo inda yan bangan ametokum da dama suka samu raunuka bayan sun shiga rabiyar fadan, wannna al'amarin ya faru ne ranar litinin.
Har yanzu ba,a san takamaiman makasudin abinda ya jawo wannan fadan ba, saidai wani daga cikin yan ametokum din yace sudai sunga lokacin da wani dan fulani ya fitar da addarsa wanda yakai sara hakan yasa wasu daga ciki suka ji raunuka.
Yan ametokum din da aka jiwa raunin sun hadar da Micheal oguntade da kuma yakini tijani, sai kuma yan bangar da aka sanar da cewa suma sunji raunuka, inda aka wuce dasu asibiti da gaggawa ana musu magani.
Bayan an tuntubi shugaban na ametokum din Col Olayinka ya tabbatar da faruwar wannan abin har yace mutanen da abin ya shafa an garzaya dasu asibiti.
Fulani da yarabawa ne suke fadan a kasuwar Aba Agudugu din sai kuma mutanen mu da suka zo rabiyar fadan inji shugaban yan ametokum din.
Saidai har ba'a sanar da sunan mutanen da suka mutu ba.
Wannan fadan yazo ne bayan an samu fadan kabilanci tsakanin hausawa da kuma yarabawa a garin Shasha a karamar hukumar akinye jihar Ibadan.
Abin lura in kuka karanta wannan labarin za kuga cewa kamar ana so ne a dorawa yan arewa domin a labarin in kuka ji zaku gane fulanin ake so a dorawa laifin.
Comments
Post a Comment