Muna Buƙatar Ƙasashen Duniya Su Haɗa Hannu Dan Kawo Ƙarshen Matsalolin Ta'addanci, Inji Shugaba Buhari a Nigeria
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci ƙasashen duniya da su tallafawa Najeriya wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ayyukan cin hanci da rashawa har ma da taɓarɓarewar tattalin arziki.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan kafafen yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar a Abuja, kamar yadda majiyar mu ta Freedom Radio ta ruwaito.
Sanarwar na bayyana cewa, shugaba Buhari ya yi wannan kira ne lokacin da yake karɓar shaidar ƙulla yarjejeniyar Diplomasiyya da wasu ƙasashen duniya.
Cikin jakadun ƙasashen da suka ziyarci fadar ta shugaban ƙasa akwai jakadan ƙasar Gambia Muhammad Njie, da na Korea ta Kudu Kim Yong-Chae da kuma na ƙasar Slovakia Tomas Felix.
Sauran sun haɗa da jakadan ƙasar Bangladesh Masudur Rahman da na Australia John Donnelly da na ƙasar Guinea Bissau Dr Jaao Butiam.
Ta cikin sanarwar Buhari yace akwai buƙatar ɗaukar mataki a tsakanin kasashen duniya domin a haɗa hannu guri guda don kawo ƙarshen matsalolin dake addabar duniya musamman ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban.
Comments
Post a Comment