WANI MATASHI KE TALLAN GORO ' ACIKIN SHIGAR MANYAN MA'AIKATA
Zubairu Ibrahim Suleiman matashi ne mai kimanin shekaru 26 da ke sana'ar sayar da Goro a yankin Nyanya da ke kusa da birnin tarayya Abuja , cikin shiga irin ta kasaitattun ma’aikatan Banki ko Lauyoyi .
Zubairu Ibrahim Suleiman Ke Nan A Cikin Shigar Kasaitattun Ma'aikatan Banki Yana Tallan Goro Zubairu Ibrahim wanda haifaffen kauyen Binawa ne da ke yankin karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna , ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa tsananin sha'awar sanya kwat da wandonta ne ya sanya shi yin shigar tare kuma da tallan Goronsa . Wannan matashi ya ce da farko ya zo garin Abuja ne domin ya fara sana'a amma rashin wadataccen jari ya sanya shi rungumar tallan Goro cikin shigar da za ta ja hankalin al'umma .
Zubairu Ibrahim Suleiman mai sana'ar sayar da Goro Ya kara da cewa a duk lokacin da mutane su ka ganshi cikin wannan shigar su kan yi zaton za shi gurin aiki ne ko wani babban ofis .
Lokacin da ake sayen Goro a gurin Zubairu A karshe ya ce babban burinsa shi ne ya koma makaranta domin cigaba da karatunsa wanda kuma rashin isasshen kudi ya taka masa birki
Comments
Post a Comment