Min menu

Pages

An damke mutane 400 dake daukar nauyin ta'addanci a Nijeriya

 JAMI'AN TSARON FARIN KAYA (DSS) SUN DAMKE MUTUM 400 DAKE DAUKAR NAUYIN TA'ADDANCI A NIGERIA.



Jami'an tsaron farin kaya na Nigeria sun bayyana cewa sun damke wasu shahararrun mutane dake daukar nauyin ta'addanci a kasar.


Mutanen wadanda aka ruwaito cewa shahararrun yan kasuwa, da masu hakar ma'adinai da yan chanji ne aka Kama da tallafa ma yan Ta'adda a Nigeria.


An bayyana cewa wadannan mutanen sun fito daga jihohi guda 7 a cikin kasar, amma saidai jihohi 4 aka bayyana ya zuwa yanzu, mutanen wadanda mafi yawa basu zaune a cikin kasar an Kama su ne a wani samame da aka kai cikin sirri.


An bayyana cewa wasu daga cikin mutanen sun fito daga jihohin Borno, Zamfara, Adamawa, da Lagos.


An bayyana cewa wasun su hamshakan yan kasuwa ne kuma masu kudi inda suke tallafawa yan ta'addan da dukkanin kayayyakkin da suke bukata.

Comments