Min menu

Pages

An samu sasanto a rikicin Dangote da BUA bayan Ganduje ya saka baki

 An samu sasanto a rikicin Dangote da BUA bayan Ganduje ya saka baki



Manyan 'Yan kasuwar Nijeriya guda biyu Alhaji Aliko Dangote Da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u sun tabbatar da za su wadata Nijeriya da Sukari. 


Wannan amincewar  ta biyo bayan zaman fahimtar juna da Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya yi tsakanin shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da shugaban rukunin kamfanin BUA, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u bisa kuskuren fahimta da suka samu akan harkokin kasuwancin su. 


Hakan ce tasa gwamnan ya gayyaci 'yan kasuwar biyu kasancewar su yan asalin jihar Kano da kuma irin gudunmawar da suke baiwa jihar Kano da kasa baki daya.


A wannan zaman da aka yi kamar yadda majiyarmu ta labarto mana, ta bayyana mana cewa; 'yan kasuwar sun tabbatar da cewa babu kamshin gaskiya akan maganar da ake yadawa cewa, Aliko Dangote ya nemi Abdussamad Isyaka Rabi'u domin su yi karin kudin sukari, inda suka tabbatar da cewa wannan zance bashi da asali.


A yayin zaman sulhun, gwamnan yana tare da Dattijo kuma hamshakin dan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ministan ciniki da masana'antu Honorabul Niyi Adebayo, wakilin Kano, Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, shugaban hukumar NEPZA Honorabul Adamu Fanda da shugaban majalisar limaman Juma'a Sheikh Nasiru Adam limamin masallacin Ahmadu Tijjani dake kofar Mata. 


Bayan tattauna muhimman batutuwa da jan hankali da Gwamna da kuma Dattijo Aminu Dantata suka yi an sami daidato da fahimtar juna tsakanin manyan 'yan kasuwar biyu inda suka yi alkawarin dinke dukkanin rashin fahimtar dake tsakanin su.

Comments