Maganar zabe a 2023 babu ita idan gwamnati bata karar da yan bindinga ba
Ba Za'a Yi Zaben 2023 Ba Matukar Gwamnati Bata Hallaka 'Yan Bindiga ba inji Sen. Abaribe
Sanata Enyinnaya Abaribe ya hasaso cewar, matukar ba'a magance 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda ba to ba za'a yi zaben shekarar 2023 cikin kwanciyar hankali Ba.
Sanatan na PDP ya baiwa gwamnatin Buhari shawarar cewar, ta gaggauta kakkabe dukkan 'yan ta'addan kasar nan ko kuma shiga layin zabe a 2023 ya gagara.
Jam'iyyar PDP ta dakatar da Kwankwaso tsawon wata uku
Sen. Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewar, cikin kankanin lokaci gwamnatin tarayya nada damar hallaka 'yan bindigar, sabida haka yana kira ga Buhari da APC cewar su cikawa 'yan Najeriya alkawullan da suka dauka na dakile hare-haren 'yan bindiga, Boko-Haram, fashi da makami, Garkuwa da mutane, yaki da cin hanci da rashawa, samarwa 'yan kasa muradun abunda suke so dadai sauran su.
Shin Ko Kuna Goyon Wannan Maganar ta Sanata Abaribe?
Ko kuma bakwa goyon bayan abinda ya fada
Comments
Post a Comment